Babbar Kotun Abuja ta aza ranar 28 Ga Afrilu cewa Shamsuddeen Bala ɗan Gwamnan Bauchi zai fara kare kan sa daga zargin ɗirka zambar kuɗi Naira biliyan 1.2 da EFCC ke yi masa a kotu.
Hukumar EFCC ce ta maka shi kotu inda ta rataya masa carbi zarge-zarge guda 20 na zamba, karkatar da kuɗaɗe, fojare da kuma laifin ƙin bayyana dukiyar sa.
Cikin watan Disamba ne PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Mai Shari’a Nnamdi Dimgba na Babbar Kotun Tarayya Abuja ya yi watsi da zarge-zarge 11 daga cikin 20 da EFCC ke yi masa, inda a yanzu saura zargi 9 kenan a wuyan sa.
Mai Shari’a ya ce EFCC ta kasa gabatar da ƙwararan hujjojin cewa Shamsuddeen Bala ya yi waɗancan laifuka 11.
Amma kuma kotun ta ce ana ci gaba da tuhumar sa kan ƙin bayyana wa EFCC adadin kuɗaɗen da ya mallaka a asusun sa na bankuna, sai kuma zamba da laifin fojare duk su na a wuyan sa.
A kan haka ne Mai Shari’a ya ce Shamsuddeen ya fito ya fara kare kan sa a cikin watan Afrilu kan tuhume-tuhume guda 9 ɗin da suka rage ake masa.
An ɗage shari’ar zuwa 28 Ga Afrilu ne bayan da lauyan da ke kare Bala mai suna Chris Uche (SAN), ya nemi a ba shi isasshen lokaci domin ya samu ya shawo kan wasu “matsalolin gida da suka sha kan sa.” Sannan kuma ya na so shi da Shamsuddeen ɗin su shirya makaman kare kai sosai. Nan take kuma mai gabatar da ƙara Wahab Shittu ya amince.
Harƙallar Sayen Gidaje: Har Yanzu Ɗan Bala Gwamnan Bauchi Na Ruwa, Kusa Da Kada:
Kotu ta ce akwai zarge-zargen wuru-wuru guda 9 a wuyan ɗan Bala, Gwamnan Bauchi.
Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ta ce akwai tuhume-tuhume guda 9 da ɗan Gwamnan Bauchi Bala Minista zai fuskanta a kotu, waɗanda su ka shafi harƙalla da wuru-wurun kuɗaɗe, waɗanda yaron ya aikata, a lokacin da mahaifin yaron ke Ministan Abuja.
A ranar Talata ce Babban Mai Shari’a Nnamdi Dimgba ya ce tuhume-tuhumen sun haɗa da laifin ƙin bayyana wa EFCC adadin kuɗaɗen da ke cikin asusun sa da ke bankuna daban-daban, zamba, da fojare.
Mai Shari’a ya ce ƙwararan hujjojin da ke gaban kotu sun sa tilas a ci gaba da tuhumar wanda ake zargin da laifuka 9 daga cikin guda 20 da a farko EFCC ta gurfanar da shi a kan su.
Mai Shari’a ya yi watsi da sauran canje-canje 11, waɗanda ke da nasaba da karkatar da kuɗaɗe, saboda EFCC ta kasa gabatar da ƙwararan hujjoji.
Haka nan kuma kotu ta sallami sauran mutun huɗu da ake tuhumar su tare da ɗan Bala. Mai Shari’a ya ce hujjojin da EFCC ta gabatar ba su kama mutanen da laifin karkatar da kuɗaɗe ba, a cikin tuhume-tuhume 11 da aka yi masu.
Ɗan Bala dai ya shiga jula-jular zargin sa da sayen kadarori na naira biliyan 1.2 a cikin Abuja, tsakanin 2014 zuwa 2015.
EFCC ta ce ya sayi gidajen a lokacin da mahaifin sa ke Ministan Abuja.
Shi ma Bala Mohammed ya na fuskantar tuhume-tuhume a kotu. An tsaida ta sa ne saboda ya samu kariya bayan an zaɓe shi Gwamnan Bauchi, a watan Mayu, 2019.
Za a ci gaba da shari’ar sa bayan ya kammala wa’adin sa na gwamna a Bauchi.