Kotu dake Kasuwan Nama a garin Jos jihar Filato ta warware auren shekara shida bayan matar Pateince Sunday ta kai karan mijinta Danjuma Musa saboda cin zarafin ta da yake yawan yi a gida.
Patience ta ce Musa ya fara cin zarafin ta bayan da suka cika shekaru hudu da aure.
“Musa na yawan duka na sannan da zargin da yake yawan mun na neman mazaje a waje.
Patience ta ce Musa ya yi watsi da al’amarin kula da ita da ‘ya’yan su da suka haifa.
Alkalin kotun Suleiman Lawal ya raba auren duk da kokarin da kotun ta yi na ganin ta sasanta ma’auratan.