• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    ZAƁEN KANO: Ganduje, Gawuna Garo da APC sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓe, sun yi zanga-zanga a Kano

    Ba ayi zabe a Katsina ba, coge aka yi kuma za mu garzaya Kotu – Lado-Danmarke

    Hyacinth Alia na APC ya lashe zaben gwamnan jihar Benuwai

    Umar Bago na APC ya lashe zaben gwamnan Neja

    KURUNKUS: Abba Gida-Gida ya doke ɗan takaran Uban Abba, Gawuna na APC da kuri’u sama da miliyan ɗaya a Zaɓen gwamnan Kano

    ZAƁEN GWAMNAN JIGAWA: Namadin APC ya natsar da Lamidon PDP a Jigawa, ya lallasa shi da kuri’u 618,449

    Thugs-attack-collation

    ZAƁEN GWAMNONI YA ƊAU ZAFI: An kashe shugaban PDP bayan an lakaɗa masa dukan tsiya a rumfar zaɓen sa

    2023: Ya mutan Adamawa, ga Tinubu ga Binani na kawo muku su – Shelar Buhari a Yola

    ADAMAWA TA KWASHI ‘YAN KALLO: Binani ta kamo hanyar tururmusa ƙarti 14 a kokawar ƙwace kujerar gwamna

    ZAƁEN GWAMNAN ANAMBRA: Muhimman Abubuwan Da Suka Faru Daga Ƙarfe 11 Zuwa 12:30 Na Ranar Zaɓe

    INEC ta dage zabe a rumfuna 10 a jihar Legas

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

No Result
View All Result

Zamfarawa sun yi ƙorafi kan yadda Gwamna Matawalle ke tsallen-gada bisa rahoton kwamitin da ya bankaɗo masu laifi a kashe-kashen jihar

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
February 10, 2022
in Labarai daga Jihohi
0
Gwamna Matawalle ya bai wa Majalisar Dokoki da Kotunan Zamfara ‘yancin gashin kan su

Al’ummar Jihar Zamfara na ci gaba da nuna damuwar su kan yadda Gwamna Bello Matawalle ya ƙi yin amfani da shawarwarin Da Rahoton Kwamitin Musabbabin Rikicin Zamfara Da Yadda Za A Magance Shi a jihar.

Kwamitin dai a cikin 2019 ne Gwamna Matawalle ya kafa shi da kan sa, wanda aka ɗora tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar a matsayin Shugaban Kwamiti. Kwamitin ya miƙa wa gwannan rahoton abin da ya bankaɗo, kuma ya lissafa waɗanda ke da hannu, yawan asarar da aka yi, waɗanda aka kashe da waɗanda aka raba da gidajen su. Hatta yawan marayu da zawarawa mata da masu takabar da aka mutu aka bari, duk kwamitin ya lissafa.

Kuma ya lissafa waɗanda za a hukunta, saboda samun su da haɗa baki da ‘yan bindiga. Tun cikin Oktoba 2019 kwamitin ya miƙa wa gwannan rahoton sa.

Yayin da Gwamna ke cewa ya yi aiki da wasu shawarwari da kwamitin ya bayar, al’ummar Zamfara na cikin halin nuna rashin yarda da hakan. Su na zargin gwamnan ya na tuma tsallen gada kan rahoton, ya na tattake shi.

PREMIUM TIMES a cikin 2019 ta buga labarin kwamitin ya ce ya yi nazarin lamarin ‘yan bindiga a Jihar Zamfara, tun daga Yuni 2011 zuwa Mayu 29 na shekarar 2019, ranar da Matawalle ya kama mulki.

Daga 2011 zuwa 2019 ɗin kuwa, duk lokacin tsohon Gwamna Abdul’aziz Yaro ne da Matawalle ya gada.

Matawalle ya kafa kwamitin a lokacin da ya ke cikin jam’iyyar PDP. Sai dai kuma a yanzu ya na cikin jam’iyya mai mulki, wato APC.

A lokacin da aka damƙa masa rahoton, Abubakar Shugaban Kwamiti ya ce tsakanin 2011 zuwa Mayu 2019 matan aure 4,983 sun rasa mazajen su, waɗanda ‘yan bindiga suka kashe.

Kwamitin ya ce a wadancan shekaru an samu yaran da aka maida marayu su 25,050. Sannan kuma an raba mutum 190,340 daga gidajen su.

Rahoto ya ci gaba da nuna cewa Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba sun rasa shanu 2,015, tumaki 141, jakai da raƙuma 2,600 sai kuma an yi asarar motoci da babura da sauran ƙananan ababen hawa 147,800 waɗanda aka banka wa wuta a yankuna daban-daban na jihar Zamfara.

Kwamiti ya ci gaba da cewa an yi asarar naira biliyan 3 waɗanda aka riƙa biyan ‘yan bindiga a matsayin kuɗin fansar waɗanda su ke yin garkuwa da su. An kuma yi garkuwa da mutum 3,672 a shekarun.

Haka kuma kwamitin ya kama sarakuna 5 da laifi, hakimai 33 da dagatai. An kuma samu wasu sojoji 10 da ‘yan sanda sun haɗa baki da ‘yan bindiga.

Yayin da ya ke karɓar rahoton, Matawalle ya yi alƙawarin zai yi amfani da shawarwarin da ke cikin sa, ba tare da wani abu ya ɗauke masa hankali daga aikata hakan ba.

Yayin da su ke tattauna batun a shafin ta na Tiwita, fitacciyar ‘yar jaridar nan wadda kuma ‘yar asalin Zamfara ce, Kadria Ahmed ta yi kira ga Gwamna Matawalle ya yi aiki da rahoton.

Ta ce rashin yin aiki da shawarwarin da kwamitin ya bayar koma-baya ne ga tsaron jihar Zamfara.

Shi kuwa Yahuza Getso, wani mai nazarin harkokin tsaro da tashe-tashen hankula, cewa ya yi shi kan sa kwamitin ma duk bige ce kawai.

“Abin da aka saki har jama’a suka sani a rahoton ai cikin cokali ne. Mun sha tambayar Gwamna ya ba mu rahoton ko kuma ya sa a buga shi a jaridu domin mu bi shi a tsakane, amms sun ƙi ba mu.

“Ni na san dama ba za a fitar mana da sakamakon binciken da kwamitin ya yi ba. Saboda akwai hukuncin da gwamnati ba ta iya ɗauka. Ko kuma akwai abin da ba ta so mu sani.”

Ita ma wata ƙungiya mai suna Zamfara Circle Initiative ts yi kira ga gwamnatin Zamfara ta yi aiki da rahoton kwamitin. Haka shugaban ƙungiyar mai suna Al-Amin Tsafe ya shaida wa wakilin mu.

Ya ce ƙin yin aiki da rahoton babbar illa ce ga tsaron jihar Zamfara.

Shi ma wani babban malamin jami’a a Jami’ar Usmanu Danfodiyo mai suna Tijjani Shinkafi, wanda ɗan jihar Zamfara ne, ya ce idan aka yi amfani da rahoton kwamitin, to hakan zai faranta rayukan al’ummar yankunan da bala’in ya fi shafa.

Daraktan Yaɗa Labarai na Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai na Zamani, na Gwamna Matawalle mai sun Ibrahim Zauma, ya ce masu sukar Gwamna kan wannan lamari ba su yi masa adalci ba.

Yayin da ya ce Matawalle ya fara aiki da wasu shawarwarin da kwamitin ya bayar, ya ce wasu shawarwarin kuwa Gwamnatin Tarayya ce kaɗai za ta iya aiwatar da su.

Tags: AbujaHausaLabaraiNajeriyaNewsPREMIUM TIMESZamfarawa
Previous Post

Yadda mai bada shaida ya fallasa yawan kamfanoni da maka-makan gidajen da tsohon Shugaban Hukumar NECO da JAMB ya mallaka

Next Post

BUGUN-MUZURUN-SHEKU: Masu hannu wajen shigo da gurɓataccen mai za su girbi abin da su ka shuka -Buhari

Next Post
Zan samar wa duk wani dan Najeriya tsaro daga ‘yan bindiga da mahara a duk inda yake – Buhari

BUGUN-MUZURUN-SHEKU: Masu hannu wajen shigo da gurɓataccen mai za su girbi abin da su ka shuka -Buhari

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Nan ba da dadewa ba zan mutu don na kammala abinda ya zo dani duniya – Fasto Odumeje
  • AZUMIN RAMADANA: Coci ta rabawa musulmai matalauta kudade da abinci a Kaduna
  • Talakawa na cikin tsananin rashin ruwa a Kaduna – Bukatar ‘Yan kaduna na farko ga Uba Sani, Sabon Gwamna
  • Yadda Hukumar zabe ta Kakkafci kuri’u na, ta lallafta wa Tinubu ya ci zaɓe – Atiku
  • ALƘAWARIN ABBA GIDA-GIDA GA KANAWA: ‘Ba zan yi wasa da damar da ku ka ba ni ba’

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.