A ranar Alhamis da safe ‘yan bindiga sun afka kauyen Rogoji a karamar hukumar Bakura inda suka kashe mutum biyar a kauyen.
Mazauna kauyen sun ce ‘yan bindigan sun afka kauyen ne saboda yadda mazauna kauyen suka hada kai da jami’an tsaro da kungiyar ‘yan sa kai domin kai musu hari.
Mazauna kauyen sun bayyana wa jami’an tsaro da ‘yan kungiyar sa kai tsarin aiyukkan da ‘yan binda ke yi a Lambar Bakura zuwa Dogon Karfe inda hankan ya sa jami’an tsaron suka afka musu.
Wani mazaunin Bakura Hamza Abdullahi ya ce maharan sun afka kauyen yayin da ake sallah asuba.
Abdullahi ya ce ‘yan bindiga sun kashe mutum biyar a kauyen duk da arangamar da suka yi da ‘yan bangan yankin.
Wani mazaunin Rogoji, Bello Mande ya ce a ƙasa ya tsere zuwa Lambar Bakura kafin ya samu motan zuwa Talatan Mafara a lokacin da ‘yan bindigan suka kawo wa kauyen su hari.
“Daga ba Dan kokarin da ‘yan sa kai suka yi ba da ‘yan binda sai sun yi wa kowa sata a kauyen.
Mande ya ce gudun kada ‘yan bindigan su sake dawowa kauyen ya sa mazauna kauyen ke tserewa duk da cewa an samu zaman lafiya a kauyen.
“Tun farko abin da ya faru shine wasu mazauna kauyen da suka san tsarin aiyukkan ‘yan bindigan sun je suka fada wa jami’an tsaro sirrin yan bindigan. Daga nan kuma sai wasu a kauyen dake da alaka da ‘yan bindigan sai suka je suka fada wa ‘yan bindigan cewa daga kauyen mu ne aka je aka tona asirin su wajen jami’an tsaro.
“Ina da tabbacin cewa ‘yan bindigan za su sake dawowa domin kafin su tafi sun bar sakon cewa za su dawo.
Mande ya ce an yi jana’izar mutum biyar din da ‘yan bindiga suka kashe da yamman Alhamis.
Discussion about this post