Wani abin tashin hankali da ya auku a jihar Zamfara ranar Juma’a shine yadda ƴan ta’addan ƴan bindiga suka afka ƙauyukan wasu kananan hukumomin jihar suka kashe mutum sama da 30 sannan suka sace mata da dama.
Maharan sun kai hari waɗannan ƙauyuka ne saboda mutanen garuruwan sun gaza biyan naira miliyan 40 kuɗin haraji da ƴan ta”addan suka ƙaƙaba musu.
Ƙauyukan sun haɗa da Nasarawar Mai Fara, karamar hukumar Tsafe, Yar Katsina, ƙaramar hukumar Bungudu da ƙauyen Nasarawa dake ƙaramar hukumar Bakura.
Idan ba a manta ba a baya ƴan bindiga sun aika da wasiku wasu ƙauyuka inda suka gargaɗi mazauna ƙauyukan su biya kuɗin haraji da suka ƙaƙaba musu na miliyoyin naira.
Gogarma Ada Aleru ne ya saka wa mutanen waɗannan ƙauyuka harajin dole. Da basu iya biya ba kuma ya aika da su lahira ya kuma sace matayen su da yawa ya nausa da su cikin daji.
A ƙauyen ƴar Katsina maharan sun tarwatsa masallata ne a masallacin Juma’a. A nan sun kashe mutum 10 baya ga mata da yara ƙananan da suka gudu cikin daji. Wasu kuma suka faɗa hannun ƴan bindiga.
Wani ma’aikacin lafiya ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa yana ƙauyen a lokacin da mahara suka dira.
” Abin dai ba a cewa komai domin na ga mata da yara ƙanana suna gudun tsira cikin daji. Nima arcewa muka yi zuwa yankin Raɓah dake jihar Sokoto.