Sanin kowa cewa gwamnan Oyetola na jihar Osun da minista Rauf Aregbesola sun saka kafar wando daya tun bayan sabulewa daga tafiyar gwamnan da minista Aregbesola yayi.
Gwamna Oyetola dai dan uwan tsohon gwamnan jihar Legas ne Bola Tinubu wanda shine Aregbesola ya mika wa ragamar mulki bayan ya kammala wa’adin mulkin sa a jihar Osun.
A wannan karo sai Aregbesola ya fidda dan takara wanda yake so ya kada Oyetola na bangaren Tinubu kuma gwamna maici.
Jam’iyyar APC ta gudanar da zaben fidda gwani ranar Asabar kuma gwamna Oyetola ne yayi nasara a zaben inda ya doke Moshood Adeoti da kuriu 222,169, shikuma Adeoti ya samu kuriu 12,000 kacal.
Sai dai kuma minista Aregbesola ya ce bangaraensa ba su yarda da zaben ba, yana mai cewa za su ci gaba da yin nazarin sakamakon zaben nan ba da dadewa za su bayyana matsayin su.
Discussion about this post