Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce ya zuwa ranar Litinin da ta gabata an samu mutum 5,353,744 da su ka yi rajistar katin zaɓe da ake gudanarwar yanzu.
Hukumar ta bayyana haka ne a cikin rahoton mako-mako da ta ke bayarwa na kwata ta 3 mako na 4 a Abuja a ranar Litinin.
Haka kuma INEC ta bayyana cewa mutum 2,805,089 da su ka yi rajista sun kammala rajistar ne ta yanar gizo da gani da ido, wanda daga cikin su mutum 1,148,631 ne su ka yi rajista ta hanyar yanar gizo yayin da kuma 1,656,458 su ka yi ta hanyar ido da ido.
Ta ƙara da cewa nazarin jinsin masu rajistar da su ka kammala rajista ya nuna cewa mutum 1,414,675 maza ne, sannan 1,390,414 mata ne, yayin da 25,523 naƙasassu ne.
Rahoton ya kuma nuna cewa Hukumar Zaɓen ta karɓi takardun buƙata guda 8,919,606 na yi wa masu zaɓe sauyin wurin zaɓe da musanyar katin zaɓe da kuma ƙarin bayani game da mutum.