Shugaba Umaro Embalo na Guinea-Bissau ya yi wa manema labarai jawabin cewa fanɗararrun mahara da su ka yi yunƙurin juyin mulki a ƙasar ba su yi nasara ba, kuma ya ƙara da cewa duk an damƙe su.
Jaridar New York Times ta Amurka ce ta bayyana haka, inda ta ce juyin mulkin wanda ake yi ƙoƙarin kifar da Gwamnatin Dimokraɗiyya a ƙaramar ƙasar da ke Afrika ta Yamma.
Embalo ya ce an kashe jami’an tsaron sa da dama a ƙoƙarin da fanɗararrun su ka yi na ƙwace mulki, wanda ya ce hakan na nufin yunƙuri ne na kashe dimokraɗiyya a Guinea-Bissau.
“Ba yunƙurin juyin mulki kaɗai aka yi ba. Fanɗararrun sun yi niyyar kashe Shugaban Ƙasa ɗungurugum da Firayi Minista da sauran ministoci na baki ɗaya.”
“Fanɗararrun mahara ɗauke da muggan makamai sun nemi kutsawa cikin ginin, amma aka kore su. Sun yi kyakkyawan shiri, kuma mutane ne masu amfani da muggan ƙwayoyi.” Cewar sa.
Jawabin shugaban ya zo ne bayan da sojoji su ka yi amfani da manyan makamai suka kori maharan da suka nemi yin amfani da karfin tsiya su shiga wurin da shugaban ke taro da ministocin sa.
Afrika na fama da matsalar juyin mulki, inda daga 2020 aka yi yunƙurin juyin mulki sau shida
Discussion about this post