Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kai karan wani matashin mai shekara 18 Mamma Aminu kotun dake Gwagwalada bayan ta kama shi da laifin sace kujeru da karafa a wata makarantar firamare a Abuja.
Dan sandan da ya shigar da karar Abdullahi Tanko ya ce rundunar ta kama Aminu bayan wani dan kungiyar ‘yan sa kai Yahaya Mohammed ya kawo karar ofishinsu ranar 12 ga Fabrairu.
Tanko ya ce Aminu da wasu abokansa da suka gudu sun saci kujeru da karafuna da kudin su ya kai naira 60,000 a makarantar firamaren ‘Pilot science school’ Gwagwalada.
Ya ce yayin da suke gudanar da bincike jami’an tsaron sun kwato sauran karafunan da Aminu da abokansa suka sace daga makarantar.
Sai dai kuma duk da haka Aminu ya musanta aikata haka a kotu.
Alkalin kotun Sani Umar ya bada belin Aminu akan Naira 100,000 tare da gabatar da shaida daya a gaban kotu.
Umar ya ce shaidan da Aminu zai gabatar zai kawo katin shaida ta kowace iri sannan da hotunan fasfo biyu wa rajistatan kotu.
Alkalin ya ce za a daure Aminu a kurkukun dake Suleja idan bai iya cika sharuddan da kotun ta bada.
Za a ci gaba da shari’a ranar 23 ga Maris.