‘Yan sandan jihar Ogun sun cafke wata mata da ta shahara wajen amfani da jabun kudi tana damfaran mutane a kasuwannin jihar Ogun.
Kakakin rundunar Abimbola Oyeyemi ya ce an kama wannan mata ranar Juma’a ne a a kasuwar Kila dake karamar hukumar Odeda.
Abimbola ya ce rundunar ta kama matan ranar 14 ga Faburairu bayan kungiyar masu siyar da hatsi da ‘ya’yan itatuwa a Egbalawa sun kai kara caji ofis.
Ya ce ‘yan sanda sun kama wannan mata da jabun kudaden da ya kai naira 24,000 a jakanta yayin da take ragargaza cefanenta a cikin kasuwa hankalinta kwance.
Sakamakon binciken da ‘yan sanda suka yi ya nuna cewa wannan ba shine karon farko da ‘yan sanda ke kama matan da jabun kudade tana damfaran mutane a kasuwannin jihar ba.
Abimbola ya ce a ofishinsu matan ta bayyana wa ‘yan sanda cewa takan hada jabun kudi da na gaske wajen siyan kaya a kasuwa.
Kwamishinan ‘yan sanda jihar Lanre Bankole ya ce fannin gurfanar da masu aikata laifi irin haka ne za ta ci gaba da gudanar da bincike.