A daren Litini ne ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sanda uku a jihar Ebonyi.
Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun harbe ‘yan sandan a kofar shiga ginin ofishin ‘yan sanda dake hanyar Enugu zuwa Abakaliki.
Majiyar ta kara da cewa ‘yan sandan sun gamu da ajalinsu ne a wajen aikin binciken motoci a wani shinge da suka kafa. Bayan sun yi kokarin dakatar da wata Bas da ke cike makil da ‘yan bindiga basu sani ba sai suka bude musu wuta.
Kakakin rundunar Loveth Odah ita ma ta tabbatar da aukuwar wannan mummunar abu. Ta ce tuni har an ajiye gawarwakin dakin ajiye gawa dake asibitin Abakaliki.
Loveth ta ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran barnar da ‘yan bindigan suka aikata.
A makon da ya gabata ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda da dama a shingayen tsaro a jihar Enugu.
Sakamakon bincike ya nuna cewa wannan ba shine na farko ba da ‘yan bindiga ke kashe ‘yan sanda a yankin Kudu maso Gabashin kasar nan ba.
Kungiyar IPOB ne aka fi samu da laifin kashe jami’an tsaro a wannan yanki sai dai wannan karo babu wanda aka kama da laifin aikata haka.
Nnamdi Kanu, wanda shi ne Shugaban Ƙungiyar IPOB masu rajin ɓallewa daga Najeriya ko da tsiya na gurfane a kotu saboda laiffukan da suka hada da cin amanar ƙasa, yi wa ƙasa zagon-ƙasa, maƙarƙashiya da kuma ayyukan ta’addanci.
Discussion about this post