‘Yan bindiga sun kai farmaki a kauyukan dake kananan hukumomin Bakori da Funtua a jihar Katsina inda suka kashe mutum 13 sannan suka yi garkuwa da mutane da dama a ranakun Litinin da Talata.
Kauyukan da ‘yan bindigan suka kai wa hari sun hada da Guga, Gidan Kanawa da Dukawa dake da iyaka da jihar Kaduna.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ‘yan bindiga sun kashe dagace da wasu mutum hudu a kauyen Yan gayya da wasu mutum 12 a kauyen Ilela.
Wani mazaunin kauyen Guga Nafiu Muhammadu ya bayyana cewa ‘yan bindigan sun yi garkuwa da dagacen kauyen Alhaji Umar kuma sun kashe wasu mutum 10.
“Maharan sun shigo suna ta harbe-harbe bayan haka sun cinna wa shagunan mutane wuta.
“Garin gudun tsira da mutane suka rika yi sai ‘yan bindigan suka rika harbin mutane da yayi sanadiyyar mutum 10 nan take.
“Dagacen kauyen na da daman guduwa amma sai ya dawo yana cewa mutane su gudu. Hakan ya sa ‘yan bindigan suka kama shi suka mai da shi gidan sa suka kwashi abinci da kudi.
Muhammadu ya ce maharan sun tafi da dagacin.
Sannan har yanzu ba a yi jana’izan mutum 10 din da suka rasu ba.
Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a daren Litini ne ‘yan bindigan suka far wa kauyen Dukawa.
Majiyar ya ce ‘yan bindigan sun bi gida-gida suna neman abincin kwashewa.
“Da basu samu abin da suke so ba sai suka yi garkuwa da mata takwas da yara shida daga kauyen.
“Zuwa yanzu an fara tattaunawa da ‘yan bindigan domin jin yadda za ceto wadanda suka sace.
Daga nan sai ‘yan bindigan suka far wa kauyen Gidan Kanawa bayan sun fice da kauyen Dukawa.
Wani mazaunin kauyen Attahiru Bala ya ce ‘yan bindigan sun kashe mutum uku a kauyen.
Discussion about this post