Akalla mutum 62 ne ‘yan bindiga suka kashe a kasar nan a cikin makon jiya daga ranar 20 zuwa 26 ga Fabrairu.
Jami’an tsaron guda 9 wanda a ciki akwai ‘yan sanda 4, jami’an NSCDC 4 da jami’in NDLEA daya na daga cikin jami’an tsaron da aka kashe sannan da mutum 53 farar hula.
An samu karuwa a yawan mutanen da aka kashe a makon daya gabata inda a wancan mako an kashe mutum 49, ‘yan sanda uku ne.
Bisa ga rahotannin da gidajen jaridu suka buga an kashe wadannan mutane a shiyyoyi biyar daga cikin shiyyoyi shida a fadin kasar sannan.
Jihar Ebonyi
‘Yan bindiga sun harbe mutum daya cikin jami’an hukumar NDLEA dake aiki a hanyar Enugu zuwa Abakaliki ranar Lahadin da ya gabata a jihar Ebonyi. Wani daga cikin jami’an ya ji rauni a jikinsa a dalilin harin.
Jihar Anambra
‘Yan bindiga sun kashe wani babban dan kasuwa kuma shugaban kamfanin ‘Ofoma Associates Limited’ Gab Ofoma ranar Lahadi.
Ofoma Dan asalin kauyen Umunnealam, Umudim, Nnewi ne. ‘Yan bindiga sun tare motarsa yayin da yake hanyar komawa gidansa dake garin Fatakwal.
‘Yan bindigan sun kashe Ofoma a hanyar Ukpor zuwa Mbosi.
Bayan haka a kauyen Ebenebe dake karamar hukumar Awka ta Arewa wasu ‘yan kungiyar asiri sun afka wa wasu masu bukin jana’aizar rasuwar wani dan uwan su suka kashe mutum 20.
Jihar Imo
‘Yan bindiga sun afka ofishin ‘yan sanda dake Isu a jihar Imo inda suka kashe ‘yan sanda biyu a wurin.
‘Yan sandan sun gamu da ajalinsu ne a dalilin bama-baman da ‘yan bindigan suka rika hurgowa cikin ofishin ‘yan sandan.
Jihar Niger
‘Yan bindiga wanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun kashe jami’an hukumar NSCDC guda hudu a kauyen Galadiman Kogo dake karamar hukumar Shiroro.
Maharan sun kashe mazauna garin mutum 6 a harin da suka yi a daren ranar Lahadi.
Bayan haka ‘yan bindiga sun kashe mutum 18 inda a ciki akwai Uba da da a kananan hukumomin Mashegu, Lavun da Wushishi.
Mutane da dama sun zama ‘yan gudun hijira a dalilin harin da ‘yan bindigan suka yi tsakanin ranar Juma’a da Asabar din da suka gabata.
Jihar Osun
Akalla mutum biyu ne suka rasa rayukan su a harin da ‘yan bindiga suka yi a taron jami’iyyar PDP da aka yi a kauyen dake karamar hukumar Iwo ranar Laraban da ya gabata.
Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce ‘yan jagaliyan siyasa ne suka kashe daya daga cikin mutanen da suka mutu a taron Toib Mutallib
Jihar Edo
A ranar Alhamis din da ya gabata ne ‘yan bindiga suka kashe ‘yan sanda biyu da mutum biyar a jihar Edo.
‘Yan bindigan sun kashe mutanen ne yayin da suka afka bankina hudu sannan ‘yan sanda biyu bayan sun Kai hari a ofishin ‘yan sanda duk a garin Uromi dake karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas.
Jihar Taraba
‘Yan bindiga sun kashe daya daga cikin hadiman gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku, Levi Gbashi a karamar hukumar Donga.
Gbashi ya gamu da ajalinsa a wajen jana’iza a kauyen Ityopaa ranar Asabar.
Discussion about this post