Mahara sun kashe ‘yan sanda uku ciki har da DOP A Rano a harin da suka kai kauyen Magama dake karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina Ranar Talata.
Majiya da dama sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindiga sun shigo kauyen da misalin karfe 3 na dare inda suka yi batakashi da ‘yan sanda da kungiyar ‘yan banga har na tsawon awayi uku.
Wani jigo a jami’iyyar APC a kauyen ya ce ‘yan bindigan sun shigo kauyen ne domin su yi garkuwa da iyalin babban dan kasuwa Mustapha Danye dake zama a Magama.
Jigon ya ce ‘yan bindigan sun shiga gidan Danye kuma sun sace matar sa da ‘yarsa amma makwabta sun yi gaggawan kiran jami’an tsaro da ‘yan kungiyar sa kai.
Ya ce DPO Rano ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake hanyan zuwa kawo wa ‘yan sandan dake bata kashi da ‘yan bindigan taimako.
” ‘Yan bindigan sun yi wa motar da DPO ke ciki zobe suka buda musu wuta. Nan take DPO Rano ya rasu tare da wasu ‘yan sanda biyu da wani mutum daya sannan sojoji biyu sun ji rauni.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isa ya tabbatar da rasuwan ‘yan sandan.
Isa ya ce jihar na yawan samun hare-haren ne saboda yadda ‘yan bindiga suka gudo daga jihohin Zamfara da Sokoto saboda ruwan bama-baman da jami’an tsaro ke yi a jihohin.