‘Yan bindiga sama da 200 bisa babura sun kashe dagacen kauyen Yangayya dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina Jafaru Rabiu tare da wasu mutum hudu.
Wani mazaunin kauyen Halilu kabir ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun dira kauyen su da misalin 12 na dare.
“Daga shigarsu sai suka yi kan mai uwa dawabi da harbi ta ko Ina inda kowa cikin tsoro a kauyen ya ruga gidan dagacen domin samun mafaka
“Maharan sun shiga gida-gida suna yi wa mutane sata sannan suka kashe wasu mutune hudu.
Wani cikin ‘yan uwan marigayi Rabiu Ibrahim Safiyanu ya ce ‘yan bindigan sun harbe dagacen a gidansa ne.
Safiyanu wanda ke zama a cikin garin Katsina ya ce sun sanar wa ‘yan sanda harin da ‘yan bindigan suka kai kauyen.
Bayanai sun nuna cewa ‘yan bindigan da suka afka kauyen Yangayya daga dajin Dankarami suke kuma suna daga cikin wadanda suka yo hijira daga yankin jihar Zamfara saboda ragargazarsu da zami’an tsaro su ke yi a can.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Gambo Isa ya tabbatar da harin.
Isa ya ce rundunar ‘yan sandan sun ceto wasu da aka sace daga kauyen da dabbobi da dama a maharan suka sace.
“Bayan haka rundunar ‘yan sandan dake Jibia sun yi gaggawar kai dauki kauyen inda suka ceto wasu mutanen da dabbobin da suka sace a hanyar su na zuwa cikin kungurmin dajin Dumburum.
Isa ya ce ‘yan bindigan da suka buwayi mutane a Jibia, Batsari, Safana da Danmusa duk daga jihar Sokoto suka yi kaura suka shigo jihar Katsina.
Harin da ‘yan binda suka yi a kauyen Yangayya ya auku ne kwanaki kadan da ‘yan bindiga suka kashe mutum 12 a kauyen Illela a karamar hukumar Safana.
Kafin haka ‘yan bindiga sun kashe mutum 50 a kauyen Ruwan Godiya dake karamar hukumar Faskari.