Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce shi da wasu gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma shirin sayo jirage masu tuka kansu daga kasar Turkiyya domin magance matsalar ‘yan bindiga yaki ci yaki cinyewa a yankin.
Gwamna El-Rufai ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da BBC Hausa ranar Alhamis.
El-Rufai mya kara da cewa gwamnonin sun dauki wannan mataki ganin cewa magance matsalar rashin tsaro a dazukan yankin ya kai sojoji da sauran jami’an tsaron Najeriya dare, haryanzu ba a gano bakin zaren ba.
A dalilin haka gwamnan yace da shi sa wasu gwamnonin jihohi biyar na yankin suka yanke shawarar shigowa da jirage da ake tuka su daga kasa da na’ura wadanda ake dora musu makamai da ake iya sarrafawa daga nesa daga kasar domin taimaka wa sojojin saman Najeriya wajen murkushe su.
“Gwamnatin Turkiyya tana da wasu drone wato jiragen yaki da ake tuka su daga kasa da na’ura masu daukar bam da rokoki, kuma mu gwamnatocin wadannan jihohi guda shida dama mun yi shiri za mu je Turkiyya mu zauna da shugabannin kamfanonin kasar mu sayo su, mu bai wa sojojin saman Najeriya su yi amfani da su,”
Gwamnan ya ce matsalar ta’addanci ta zarce duk yadda ake tunani kuma ‘yan bindiga suna samun makudan kudade don haka akwai bukatar a yi musu kifa daya kwala a gama da su.
Ya ce sun san inda ‘yan bindigar suke zaune amma “abin da ya hana a kai musu farmaki shekarun nan shi ne rashin samun damar a kira su ‘yan ta’adda kamar yadda aka yi wa Boko Haram…amma tun da yanzu kotun tarayya ta ce sojoji za su iya kashe su ba tare da an ce an kashe farar hula ba.”