A farkon wannan mako ne wani matukin a daidaita sahu mai suna Chinenye ya bindige abokin aikinsa har lahira saboda kwanan shinkafa ‘rangen’ a gidan abinci a jihar Abia.
Wannan abin tashin hankali ya auku ne a kauyen Owerri-Aba dake karamar hukumar Ugwunagbo.
Kakakin rundunar ƴan sanda Geoffrey Ogbonna wanda ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba a garin Umuahia ya ce Chnenye da kansa ya kai kansa ofishin ƴan sanda bayan ya bindige abokin sa.
Ogbonna ya ce a ranar da abin ya auku shi Chinenye ya tada balli a gidan siyar da abinci inda dandalin cin abincin ‘yan keke Napep ne, wai shi dole a bashi abinci nan take ko ya tarwatsa wurin gaba ɗaya.
“Jin haka sai dandazon masu cin abinci sula taru kaf ɗin su su ka lakaɗa masa dukan tsiya, sannan suka kora shi daga wannan gida.
” Bayan haka ne fa sai Chinenye ya koma gida ya dauko bindigar sa ya dawo shagon tare da wani abokinsa akan babur. Yana isa sai ko ya samu wani Oberagu ya dirka masa harsashi a ciki.
Ya ce an yi gaggawar kai Oberagu asibiti amma ko da aka kai shi likitoci suka tabbatar ya rasu.
Obonba ya ce matasan kauyen bayan sun ji labarin abin da ya faru sai suka cinna wa gidan Chinenye wuta.
Ya ce rundunar za ta ci gaba da bincike sannan za ta kai Chinenye kotu bayan ta kammala.