Sakamakon bincike ya nuna cewa talauci, rashin tsaftace muhalli da rashin wayar da kan mutane na daga cikin matsalolin da ya sa ke samun yaran dake fama da tsananin yunwa a Abuja da sauran jihohin Najeriya.
Matsalar yunwa a jikin yara ya ci gaba da yaduwa duk da tsauraran matakan da gwamnati da kungiyoyin bada tallafi daga ƙasashen waje kamar su UNICEF da DFID suka dauka a kasar nan na bada kudade masu yawa.
Daya daya cikin matakan kawar da yunwa a jikin yara da UNICEF, DFID da gwamnati suka dauka sun hada da ciyar da yara abinci mai sunan ‘Ready-to-Use Therapeutic Food (RUTF)’.
RUTF abinci ne da ake hada shi da nikakken gyada, garin madara, siga da sauran sinadarin inga jiki wanda ke inganta jikin yara masu fama da yunwa.
Sakamakon binciken da ‘Nigeria Demographic and Health Survey’ ta yi a shekaran 2018 mata 512 daga cikin mata 1,000 ne ke mutuwa wajen haihuwa a Najeriya duk shekara sannan mata akalla kashi 17% ne ke amfani da dabarun bada tazaran haihuwa na zamani da na gargajiya a Najeriya.
Binciken ya kuma nuna cewa jarirai akalla kashi 39% daga cikin jarirai 1000 da aka haifa a shekarar ke mutuwa sannan a shekara yaro daya cikin yara takwas na mutuwa kafin ya cika shekara biyar a Najeriya.
Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya ce matsalar yunwa a jikin yara ya dade yana ci wa Najeriya tuwo a kwarya inda yara ‘yan ƙasa da shekara biyar kashi 37% ke fama da rashin girman jiki Wanda hakan ya sa ake da Yara miliyan 12 dake fama da wannan matsala.
Ehanire ya ce ya kamata gwamnati ta hada hannu da gidajen jaridu domin wayar da kan mutane sanin mahimmancin ciyar da ‘ya’yan su abincin da zai inganta garkuwar jikinsu, tsaftace muhalli da samun lafiya na gari.
Ya ce yin haka zai taimaka wajen dakile matsalar yunwa a jikin yara kanana.