An ƙiyasta cewa a duk shekara ɓarayin ɗanyen mai na satar na dala biliyan 4 kwatankwacin Naira Tiriliyan 1.7.
Kenan adadin kuɗin man da ake sacewa ya haura kuɗaɗen shigar da jihohin yankin Neja-Delta su 9 ke samu na cikin gida (IGR) da kashi 31 bisa 100.
Rahoton binciken da BudIT ta fitar cikin 2020 ya nuna jihohin Neja-Delta sun tara jimillar Naira Tiriliyan 1.3 a matsayin kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Shugaban Hukumar Kula da Haƙo Ɗanyen Mai Ta Ƙasa, Gbenga Komolafe ne ya shaida haka a cikin makon da ya gabata.
A cikin wata tattaunawa da Komolafe ya yi da Bloomberg, ya ce yawan ɗanyen man da Najeriya ke haƙowa ya tafi da kashi 25 bisa 100. Wato a kullum ana satar aƙalla ganga 150,000 kenan.
Wannan gagarimar satar ɗanyen mai da ake yi, ta sa a yanzu Libya ce kan gaba a Afrika wajen haƙo mai, ba Najeriya ba.
To amma a yanzu Komolafe ya ce Gwamnatin Tarayya ta kokarin nunka yawan wanda ake haƙowa. Sai dai kuma ya ce ƙoƙarin da ake yi ya wuce daƙile ɓarayin mai kaɗai.
Yayin da aka fara haƙo ɗanyen mai a Najeriya, wanda ya albarkaci ƙasar, a gefe ɗaya kuma ya zame mata masifa, ta hanyar gagarimar satar kuɗin da shugabanni da masu riƙe da manyan muƙamai na siyasa da manyan ma’aikatan gwamnati ke yi fiye da shekaru 40.
Amma yanzu dai Komolafe ya tabbatar cewa, “kwanan nan za a ga canji, domin ana nan ana shirin amfani da ƙarfafan matakan tsaro.”