Watanni shida bayan ‘yan bindiga sun fasa wani sansanin sojoji da ke Ƙaramar Hukumar Maru, mszauna garin Matumji sun biya ‘yan bindiga har naira miliyan 40.7.
Jama’ar yankin sun ce sun tara wa ‘yan bindiga Naira miliyan 9.7, suka kai masu a ranar 4 Ga Faburairu. Waɗannan kuɗaɗen su ka biya na ƙarshe wannan watan.
Ana tara kuɗaɗen ne daga hannun mazauna karkarar, waɗanda mafi yawan su manoma ne a Matumji.
A cikin Satumba ne PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda ‘yan bindiga su ka fasa sansanin sojoji a Mutumji, har su ka kashe Sojojin Sama 9 da ‘yan sanda biyu da kuma sojan ƙasa ɗaya.
An kuma ruwaito cewa ‘yan bindigar sun saci makamai da dama a kafin su banka wa sansanin wuta.
Wani basaraken gargajiya a Matumji mai suna Abdulƙadir Abdullahi, ya shaida wa wakilin mu cewa an janye sojoji daga Matumji bayan da ‘yan bindiga suka yi raga-raga da sansanin.
Ya ce janye sojojin ya sa mutanen yankin ba su da wata kariya hare-hare. Tilas ta sa su ka riƙa biyan ‘yan bindiga kuɗaɗen ‘harajin zaman lafiya’.
Abdullahi ya ce garin Mutumji na da ƙauyuka 47 da ke ƙarƙashin sa masu ƙunshe a cikin Gundumar Hakimai 32 da masu unguwanni 4, Dagatai 32.
“Dukkan waɗannan ƙauyuka su na ƙarƙashin ikon ‘yan bindiga a yanzu. Idan ka na zaune ciki tilas sai ka biya haraji. Waɗanda su ke ganin ba su iya biyan harajin kuma sun yi hijira zuwa cikin jihohin Kebbi da Neja.
Basaraken gargajiyar ya bayyana ƙauyukan da aka gudu aka bari a hannun ‘yan bindiga sun haɗa da: Guru, Danfasa, Dogon-Ruwa, Tungar Baushi, Jesa, Gazamba, Fankashi, Damkofa, Maijankai da Gobirawar-Guru.
Ƙauyukan da su ka amince su ka riƙa biyan haraji kuwa sun ne: Sabon Garin-Mahuta, sun biya naira miliyan 6; Randa sun biya naira miliyan 6, Kwanar Dutse naira miliyan 10 sai Unguwar Kawo naira miliyan 5.
“Mutanen Matumji sun biya naira miliyan 4 kafin su fara girbin amfanin gona. Kwanan nan kuma a ranar Litinin waccan sun biya naira miliyan 9.7, cikon kuɗin harajin zaman lafiya.”
Ya ce waɗannan naira miliyan 40.7 da mutanen yankin su ka biya, ba su cikin maƙudan kuɗaɗen da suka riƙa biya matsayin kuɗin fansar iyalan su da aka riƙa yin garkuwa da su.
Yadda Ake Biyan ‘Harajin Zaman Lafiya’ Da ‘Yan Bindiga A Zamfara:
Basaraken ya shaida wa wakilin mu cewa sunan gogarman ‘yan bindigar yankin Matumji Lawalli Damina, wanda su ka ce shi ne babban gogarma yanzu a Masarautar Ɗansadau.
Baya ga karɓar kuɗaɗen haraji, yaran Damina su na yin garkuwa su na satar shanu.
A ranar Juma’a sun dira Matumji su ka kafa sansani cikin wata gonar mangwaro. Daga nan su ka shiga cikin gari, suka tare hanyar da ke zuwa Ɗansadau daga Matumji, su na fashi da makami da ƙwacen kuɗaɗe da kaya masu daraja.
Dama kuma a ranar Juma’a ɗin ce kasuwar Ɗansadau ke ci. Tsakanin Matumji da Ɗansadau kilomita 12.
Mazauna garin sun ce a lokacin an ƙwace babura 5 da kayan abinci daga hannun matanen Matumji masu komawa gida, daga cin kasuwar Ɗansadau.
A lokacin ne gogarma Damina ya umarci mutanen garin su tura masa wakilan su mutum biyu su same shi a Farar Doka cikin Mazaɓar Dangulbi. Amma kuma basaraken garin ya tura masu mutum biyar, har da wani Bafulatani Alhaji Garba, da ke zaune a wajen garin Matumji.
“A wurin taron sulhun, Damina ya umarci mazauna yankin Matumji su haɗa masa naira miliyan 50 domin ya raba wa yaran sa, kowa ya yi bushasha. Kuma idan su ka bayar da kuɗaɗen, to ba za a sake kai masu hari ba. A ƙarshe dai aka cimma yarjejeniyar cewa za su biya naira miliyan 20.”
An shaida wa wakilin mu cewa a duk lokacin da ‘yan bindiga ke son a yi sulhu, a riƙa biyan su haraji, su ka yi garkuwa da wani ne. A lokacin da aka biya kuɗin fansar sa, za su sanar da shi cewa idan ya koma gida ya wani adadin kuɗaɗen da za su riƙa biya, don kada a sake kai masu hari.
Kakakin ‘Yan Sandan Zamfara Mohammed Shehu, ya shaida wa wakilin mu cewa ba a kai masu rahoton wani yanki sun biya ‘yan bindiga naira miliyan 40.7 ba.
Sannan kuma ya ce ba zai iya magana kan batun harin da ‘yan bindiga su ka sai wa sojoji a sansanin Matumji ba, ballantana magana a kan batun kwashe sojoji daga sansanin.