A daren Talata ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mutum biyar daga cikin iyalan shugaban kungiyar malaman jami’a ASUU na Jami’ar Gusau Abdurahman Adamu.
‘Yan bindigan sun yi garkuwa da dan uwan Adamu, ‘ya’yan ‘yan uwansa biyu namiji da mace sannan da surikansa mata biyu a gidansa dake Damba Estate.
Daga nan Kuma ‘yan bindigan sun afka gidan makwabcin Adamu inda suka yi garkuwa da ma’ajin jami’ar watao ‘Bursar’ Alhaji Abbas.
Wani ma’aikacin Jami’ar ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa ‘yan bindigan sun zo da Shirin sace Adamu ne amma sai a daren Talata bai kwana a gida ba.
Zuwa yanzu dai ‘yan bindigan basu kira Adamu ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Mohammed Shehu ya bayyana wa wakilin gidan jaridar nan cewa ba shi da masaniya kan abin da ya faru.
“A yanzu Ina wurin tantance sabbin ma’aikata da rundunar ‘yan sanda za ta dauka amma da zarar na samu bayanin abin da ya faru a ofis zan sanar da ƴan jarida.
Jihar Zamfara ta yi ƙaurin suna wajen kai hare-haren ƴan bindiga da da yin garkuwa da mutane.
Har zuwa yanzu sace al’umma a jihar bai tsagaita. Jama’ar jihar har na fama da wannan matsala.
Discussion about this post