APC ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ta yi watsi da ƙa’idojin sasantawa da sharuɗɗan da kwamitin da uwar jam’iyya ta ƙasa ya gindaya domin kawo ƙarshen ruɗanin shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano.
Ɓangaren na Shekarau ya fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, a matsayin raddi da martani ga kwamitin da Shugaban APC na Riƙo na Ƙasa, Mala Buni ya kafa domin sasanta rikicin Kano.
Kwamitin Sasanta Rikicin APC a Kano, ya ƙunshi Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara da kuma Sanata Abba Ali.
Sharuɗɗan Da APCin Shekarau Ta Watsa Bola A Kano:
1. Cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai kasance jagoran APC a Kano. A matsayin sa na shugaba, ya kasance ya na nuna jagorancin tafiya tare da kowa.
2. Cewa shari’ar da suke ta kafsawa a kotu ba abin alheri ba ne, domin nan gaba babu ɓangaren da zai iya yin nasara ba tare da haɗin kan ɗaya ɓangaren ba.
3. Ganduje ya riƙa jan ɓangarorin ko’ina na jam’iyyar APC a jika, domin a gina APC da ɗimbin mabiyan ta a Kano.
4. Cewa ana jaddada wa ɓangarorin su sani sasantawa ta gaskiya, ita ce wadda aka cimma yarjejeniya ta hanyar yin sulhu. Ma’ana, babu ɓangaren da zai samu yadda ya ke so 💯 bisa 💯.
Waɗannan dai kaɗan ne daga cikin sharuɗɗan. Amma na ƙarshe shi ne Ganduje a matsayin sa na Gwamna zai kasance Shugaban Kwamitin Tuntuɓa na APC a Jihar Kano, shi kuma Shekarau ya zama Mataimakin Shugaba.
Ɓangaren Shekarau ya yi fatali da sharuɗɗan, tare da cewa kwamitin Mala Buni bai yi adalci ba.
Shekarau da sauran gaggan masu take masa baya wajen yi wa Ganduje tawaye ne suka sa hannu a takardar sanarwar yin fatali da sharuɗɗan.
Bayan Shekarau akwai Sanata Barau Jibrin, Nasiru Abduwa, Tijjani Joɓe, Sha’aban Sharaɗa, Haruna Dederi da Shehu Ɗalhatu.
Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ce ɓangaren Shekarau ya gindaya wa ɓangaren Ganduje da kwamitin sasantawa sharuɗɗan zaman lafiya.
Sanata Ibrahim Shekarau ya gindaya cewa APC ɓangaren sa ba zai amince da kwamitin shugabannin jihar da ba bisa adalci aka zaɓo su ta hanyar yin raba-daidai ba.
Ya ce ɓangaren sa ba zai amince da ɗauki-ɗora, ƙarfa-ƙarfa ko maida wani ɓangare saniyar-ware ba.
Wannan sharuɗɗa na cikin waɗanda wata sanarwa da mutum bakwai suka sa wa hannu kuma suka raba wa manema labarai a ranar Lahadi da dare.
Idan ba a manta ba dai uwar jam’iyya ta ƙasa ta gana da ɓangaren Shekarau da na Ganduje a ranar Asabar, inda aka amince cewa ɓangarorin biyu za su raba muƙamai.
Uwar jam’iyya ta ce za ta fito da tsarin yadda ɓangarorin biyu za su raba muƙamai, da kuma yadda za a tabbatar da cewa an bi ƙa’idar da aka gindaya.
Cikin sanarwar da ɓangaren Shekarau ya fitar ɗin a ranar Lahadi, ta yi kira ga mambobin jam’iyyar APC su kwantar da hankalin su tare da kasancewa masu biyayya ga jam’iyya, har zuwa lokacin da tsarin sasantawar da aka ɗauko ya kawo ƙarshe.
Waɗanda suka sa hannu a kan takardar sun haɗa da Sanata Ibrahim Shekarau na Kano ta Tsakiya, Sanata Barau Jibrin na Kano ta Arewa, Mamba Tijjani Joɓe na Rimingado/Tofa, Nasiru Gabasawa na Gabasawa da Gezawa, Haruna Dederi na Ƙaraye da Rogo, Sha’aban Sharaɗa na Birnin Kano da Shehu Ɗalhatu, Shugaban Buhari Support Group.
Sai dai kuma duk da wannan takarda da su ka fitar, sun ce har yanzu ba su yanke hukuncin matsayar da suka ɗauka ba tukunna.
Discussion about this post