• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    FALLASA RUFA-RUFAR HADI SIRIKA: Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air

    Sanata Wamakko ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi a tangaza, jihar Sokoto

    Atiku ya kafa gaggan lauyoyi 18, ya ce su tashi tsaye su ƙwato masa ‘nasarar zaɓen sa’ daga hannun Tinubu

    SHARI’AR ZAƁEN SHUGABAN ƘASA: Atiku ya zargi INEC ta ƙin ba shi kwafen bayanan zaɓe duk da ya biya haƙƙin Naira miliyan 6 kuɗin karɓar bayanan

    Gwamnatin Zamfara ta zargin tsohon gwamna Matawalle da sace motocin gwamnatin jihar da wasu kayan gwamnati

    Gwamnatin Kano ta rusa katafaren bene mai hawa uku da aka yi bisa filin gwamnati da Ganduje ya raba wa ƴan uwa da abokan arziki

    TA’ADDANCI A JIHAR NEJA: Yadda ƴan ta’adda su ka ratsa garuruwa, kafin su  kai wa sojoji da mobal farmaki

    TSAUTSAYI: Yadda ‘yan bindiga suka ware da Lami Awarware da Haulatu bayan halartar taron rantsar da Uba Sani a Kaduna

    Sojojin Najariya sun kara ragargaza wa Boko Haram motocin yaki bakwai

    Sojoji sun dagargaza matatun mai 47 sun kama barayin mai 65 – Hedikwatar tsaro na kasa

    HAJJI 2023: Yadda jirgin maniyyatan Jigawa ya koma Kano ba shiri, bayan ya samu matsala cikin sararin samaniyar Kamaru

    GANAWAR TINUBU DA NLC: Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

    QATAR 2022: Ko ƙasashen Afrika za su fidda nahiyar jin kunya a duniyar ‘yan ƙwallo

    DAGARGAZA ARGENTINA: Ƙasar Saudiyya ta ba da hutun kwana Ɗaya a wataya

    QATAR 2022: 2:1: Saudiyya ta kafa tarihin karya gadara da tutiyar buga wasan Agentina 36 a jere babu rashin nasara

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

    BIDIYO: NAJERIYA @62: Ra’ayoyin ‘yan Najeriya game da mulkin Buhari a tsawon shekaru 7 da suka gabata

    Buhari bai san ƴan ta’adda sun fidda bidiyon da suka ce sai sun sace shi da ni ba sai da na ziyarce shi – El-Rufai

    Dalilin da ya sa na raɗa wa wasu fitattun gine-gine, da titunan jihar Kaduna sunayen wasu fittattun ƴan asalin jihar

    HOTUNA: Ɗan Autan marigayi tsohon sarkin Kano Ado Bayero, Mustapha Ado Bayero, ya auri mata biyu ranar Asabar a  Kano

    BIDIYO: An yi wa ɗan takarar mu murɗiya a zaɓen fidda gwani na APC a Legas – Masu zanga-zanga

No Result
View All Result

WATSEWAR ƊAURIN TSINTSIYA A KANO: APC ɓangaren Shekarau ya yi watsi da sharuɗɗan da Kwamitin Sasantawa ya gindaya

Ashafa MurnaibyAshafa Murnai
February 8, 2022
in Rahotanni
0
WATSEWAR ƊAURIN TSINTSIYA A KANO: APC ɓangaren Shekarau ya yi watsi da sharuɗɗan da Kwamitin Sasantawa ya gindaya

Malam Ibrahim Shekarau

APC ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ta yi watsi da ƙa’idojin sasantawa da sharuɗɗan da kwamitin da uwar jam’iyya ta ƙasa ya gindaya domin kawo ƙarshen ruɗanin shugabancin jam’iyyar a Jihar Kano.

Ɓangaren na Shekarau ya fitar da wannan sanarwa a ranar Litinin, a matsayin raddi da martani ga kwamitin da Shugaban APC na Riƙo na Ƙasa, Mala Buni ya kafa domin sasanta rikicin Kano.

Kwamitin Sasanta Rikicin APC a Kano, ya ƙunshi Gwamna Bello Matawalle na Zamfara, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya Yakubu Dogara da kuma Sanata Abba Ali.

Sharuɗɗan Da APCin Shekarau Ta Watsa Bola A Kano:

1. Cewa Gwamna Abdullahi Ganduje ne zai kasance jagoran APC a Kano. A matsayin sa na shugaba, ya kasance ya na nuna jagorancin tafiya tare da kowa.

2. Cewa shari’ar da suke ta kafsawa a kotu ba abin alheri ba ne, domin nan gaba babu ɓangaren da zai iya yin nasara ba tare da haɗin kan ɗaya ɓangaren ba.

3. Ganduje ya riƙa jan ɓangarorin ko’ina na jam’iyyar APC a jika, domin a gina APC da ɗimbin mabiyan ta a Kano.

4. Cewa ana jaddada wa ɓangarorin su sani sasantawa ta gaskiya, ita ce wadda aka cimma yarjejeniya ta hanyar yin sulhu. Ma’ana, babu ɓangaren da zai samu yadda ya ke so 💯 bisa 💯.

Waɗannan dai kaɗan ne daga cikin sharuɗɗan. Amma na ƙarshe shi ne Ganduje a matsayin sa na Gwamna zai kasance Shugaban Kwamitin Tuntuɓa na APC a Jihar Kano, shi kuma Shekarau ya zama Mataimakin Shugaba.

Ɓangaren Shekarau ya yi fatali da sharuɗɗan, tare da cewa kwamitin Mala Buni bai yi adalci ba.

Shekarau da sauran gaggan masu take masa baya wajen yi wa Ganduje tawaye ne suka sa hannu a takardar sanarwar yin fatali da sharuɗɗan.

Bayan Shekarau akwai Sanata Barau Jibrin, Nasiru Abduwa, Tijjani Joɓe, Sha’aban Sharaɗa, Haruna Dederi da Shehu Ɗalhatu.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ce ɓangaren Shekarau ya gindaya wa ɓangaren Ganduje da kwamitin sasantawa sharuɗɗan zaman lafiya.

Sanata Ibrahim Shekarau ya gindaya cewa APC ɓangaren sa ba zai amince da kwamitin shugabannin jihar da ba bisa adalci aka zaɓo su ta hanyar yin raba-daidai ba.

Ya ce ɓangaren sa ba zai amince da ɗauki-ɗora, ƙarfa-ƙarfa ko maida wani ɓangare saniyar-ware ba.

Wannan sharuɗɗa na cikin waɗanda wata sanarwa da mutum bakwai suka sa wa hannu kuma suka raba wa manema labarai a ranar Lahadi da dare.

Idan ba a manta ba dai uwar jam’iyya ta ƙasa ta gana da ɓangaren Shekarau da na Ganduje a ranar Asabar, inda aka amince cewa ɓangarorin biyu za su raba muƙamai.

Uwar jam’iyya ta ce za ta fito da tsarin yadda ɓangarorin biyu za su raba muƙamai, da kuma yadda za a tabbatar da cewa an bi ƙa’idar da aka gindaya.

Cikin sanarwar da ɓangaren Shekarau ya fitar ɗin a ranar Lahadi, ta yi kira ga mambobin jam’iyyar APC su kwantar da hankalin su tare da kasancewa masu biyayya ga jam’iyya, har zuwa lokacin da tsarin sasantawar da aka ɗauko ya kawo ƙarshe.

Waɗanda suka sa hannu a kan takardar sun haɗa da Sanata Ibrahim Shekarau na Kano ta Tsakiya, Sanata Barau Jibrin na Kano ta Arewa, Mamba Tijjani Joɓe na Rimingado/Tofa, Nasiru Gabasawa na Gabasawa da Gezawa, Haruna Dederi na Ƙaraye da Rogo, Sha’aban Sharaɗa na Birnin Kano da Shehu Ɗalhatu, Shugaban Buhari Support Group.

Sai dai kuma duk da wannan takarda da su ka fitar, sun ce har yanzu ba su yanke hukuncin matsayar da suka ɗauka ba tukunna.

Tags: AbujaAPCDederiGandujeHausaKanoNewsPREMIUM TIMESShekarau
Previous Post

TSALLE ƊAYA KE JEFA MUTUM RIJIYA: Mu na da hujjojin damƙa Abba Kyari ga mahukuntan Amurka -Minista Malami

Next Post

Sauya shekar gwamna Matawalle bai saba wa dokar kasa ba – Hukuncin kotu

Ashafa Murnai

Ashafa Murnai

Next Post
Buratai ya gamsu da shirin samar da tsaro na Gwamna Matawalle

Sauya shekar gwamna Matawalle bai saba wa dokar kasa ba - Hukuncin kotu

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Ƴan sanda sun ceto yara 9 da aka yi garkuwa da su a Zamfara
  • FALLASA RUFA-RUFAR HADI SIRIKA: Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air
  • Sanata Wamakko ya yi tir da kisan kiyashin da aka yi a tangaza, jihar Sokoto
  • CIRE TALLAFIN MAI: ‘Yan Najeriya na dandana tsadar kayan abinci da motocin sufuri
  • TASHIN HANKALI: Saboda lalacewa yanzu, har Nas-Nas na fede mutum asibitoci

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.