Kwamishinan ilimin jihar Kogi Wemi Jones ya bayyana cewa gwaman jihar Kogi Yahaya Bello ne ke da hangen nesan da zai iya kawo ci gaba a kasar nan cikin duka ƴan takarar da suka bayyana ra’ayoyin su.
Jones ya fadi haka ne a jawabin da yayi a taron da aka yi a kwalejin koyar da malamai dake Ankpa.
A taron Jones ya ce babban matsalar da ya fi ci wa kasar nan tuwo a kwarya shine rashin samun shugaba mai hangen nesa kamar Yahaya Bello tun bayan samun ‘yancin kai.
“Akwai matukar banbanci game da yadda Najeriya take a da da yadda take a yanzu.
“A dalilin haka yake kira ga mutanen kasar nan da su yi kokarin gain sun kubutar da kasar daga matsalolin dake hana ƙasara samun ci gaba.
Jones ya ce Bello matashi ne wanda zai iya daukan matakan da suka kamata domin samar da ci gaba a kasar nan.
Ya mika godiyarsa game da aiyukkan samar da ci gaba da Yahaya Bello ya yi musamman a fannin ilimi a jihar.
An shirya wannan taro domin wayar da kan matasa masu zurfin tunani da manyan gobe kan yadda kasar Chana ke kokarin mai da tattalin arzikin kasar nan zuwa nata.
Maji ya ce daga shekaran 1971 zuwa 2021 kasar Chana ta karbi duka fanninin tattalin arzikin kasar ta hanyar bai wa Najeriya bashi da da bada kudin jari.
A yanzu haka kasar Chana na da kinkimakinkiman masana’antu guda 920 da suka haɗa da fannin bakin mai, layukan sadarwa, fasaha da sauran su a Najeriya.