Tsohon ɗan takarar shugaban Kasa 2019 ya bayyana cewa da shi za a fafata wajen ɗarewa kujerar gwamnan jihar Kaduna idan Nasir El-Rufai ya kammala wa’adin sa.
Datti Baba Ahmed wanda sananne a siyasar Najeriya ya bayyana cewa ya shiga jam’iyyar PDP daga APC ne domin ya yi adawa da gwamnati mai ci wanda dama can haka ya saba a ɓangaren ƴan adawa.
” Kowa ya sanni daɗaɗɗen gogarman ɗan adawa ne a siyasa. Na shiga PDP daga APC ne domin adawa, amma kuma zan ci gaba da zama a jam’iyyar idan ta iya kafa gwamnati a 2023.” In ji Datti Baba-Ahmed
” Zan ci gana da zama domin in aiwatar da ayyukan ci gaba da manufofin alkhairi da nake da shi a ƙarƙashin jam’iyyar.
Datti Baba-Ahmed ya faɗi burin sa na zama gwamnan jihar Kaduna ne a hira da yayi da Talbijin din Trust TV ranar Litinin kamar yadda jaridar ta buga.
Wannan buri na shugaban jami’ar Baze dake Abuja, Baba-Ahmed ta ci karo da burin wasu da dama daga cikin ƴaƴan jam’iyyar PDP na jihar Kaduna wanda suma sun feke wuƙaƙen su domin ganin hakan su ya cimma ruwa.
Daga cikin su akwai daɗaɗɗen ɗan jam’iyyar Isah Ashiru, wanda yayi takara a 2019.
Bayan shi akwai tsohon gwamnan jihar Ramalan Yero, sai kuma Sanata Shehu Sani da dai sauran su.
Sai dai kuma ba a nan gizo ke saƙa ba domin gwamnan jihar na yanzu Nasir El-Rufai shima ba ƙanwan lasa bane domin akwai ɗan takaran sa wanda zai tsayar ya fafata da duk wani wand PDP za ta tsayar.