Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa ‘yan bindiga sun kashe jami’an tsaro 11 da wasu mutane a tsakanin ranakun Juma’a da Asabar a kauyukan dake kananan hukumomin Shiroro da Paikoro.
Mazaunan kakanan hukumomin sun ce akalla mutum 32 ne ‘yan bindigan suka kashe.
Gwamnan jihar Abubakar Bello ya sanar da haka ranar Talata a wani takarda da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Mary Noel-Berje ta raba wa manema labarai.
Bello ya ce da rana tsaka ‘yan bindigan sama da 100 suka afka wa kauyukan inda suka kashe jami’an tsaro 11 da wasu mazaunan kauyen sannan wasu da dama sun ji rauni a jikinsu.
Ya ce jami’an tsaro sun yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘yan bindigan.
Mazauna kauyukan sun ce an kashe mutum 20 a karamar hukumar Shiroro sannan mutum daya a Paikoro da jimlar ya zama 32.
Shugaban karamar hukumar Shiroro Suleiman Chukuba ya tabbatar da rikicin da aka yi a karamar hukumar sai dai a lokacin ya ce bai da masaniyar yawan mutanen da aka kashe da yawan da suka ji rauni.
Shugaban kungiyar matasa na Shiroro Yusuf Kokki ya ce an kashe mutum 20 a karamar hukumar sannan da dama sun bace.
Gwamnan jihar Neja Sani Bello ya ce gwamnati za ta kara wa ‘yan kungiyar sakai karfi. Sannan kuma za a ci gaba da mara wa sojoji baya domin ganin sun gama da yan bindiga a fadin jihar.