Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya bayyana cewa akwai ƙwararan dalilan da za su sa a ci gaba da binciken Abba Kyari, dakataccen ɗan sandan da aka zarga da hannu a harƙalla da damfara tare da babban ɗan damfara, Hushpuppi.
Malami ya yi wannan ƙarin bayanin a ranar Litinin, lokacin da ya ke amsa tambayoyi ga Gidan Talabijin na Channels, a Abuja.
A cikin watan Yuli ne Gwamnatin Amurka ta fallasa zarge-zargen da ta ke yi wa Kyari da sauran abokan harƙallar sa.
Ramon Abbass dai da aka fi sani da Hushpuppi, ɗan Najeriya ne da mahukuntan Amurka suka damƙe a Dubai cikin watan Yuni, 2020. Tuni ya amsa laifin sa, kuma cikin wannan shekarar ce za a yanke masa hukunci.
Bayan mahukuntan Amurka sun nemi Najeriya ta ba su Abba Kyari domin ta tuhume shi, an dakatar da shi kuma ‘yan sanda suka kafa kwamitin bincike.
Sai dai kuma sun yi gum da bakin su, duk kuwa da cewa mutane na ta kururuwar a fito da sakamakon binciken a fili.
Amma kuma yanzu Malami wanda ofishin sa ne ‘yan sanda suka aika da sakamakon rahoton binciken da aka yi wa Kyari, a ranar Litinin ya tabbatar cewa “akwai hujjojin da za su sa ko dai a ci gaba da gurfanar da Kyari, ko kuma a aika shi ga mahukuntan Amurka, inda ake jiran a kai shi a tuhume shi.
Da aka tambayi Malami ko kwamiti ya kama Kyari da laifi, sai ya ce, “ai kwamiti ba zai kama wanda ya ke bincike da laifi ba. Sai dai ya fito da wasu hujjojin da za a iya amfani da su a matsayin abin dogaro kan zargin da zai kai ga gurfanar da mutum a kotu. A kotu ne za a iya kama shi da laifi, ta hanyar amfani da hujjojin da masu bincike su ka gabatar.”
Malami ya ce dalili kenan da ya da muke da wasu hujjojin da suka sa ake zargin sa.
Discussion about this post