Kai da jama’a su ka zaba ana biyanka miliyoyin kudi duk wata, ina laifi don dan talaka ya ce ka nema masa aiki?
Ban ga laifin sanata ba kan batun aure da wannan yaro ya zo masa da shi, amma na ga laifin shi kan cewa shi ba zai nema masa alfarmar samun aiki ba. Na farko dai shi ne, ita kanta zabiyar alfarmar kotu ce ta dora ta a kan kujerar sanatan.
Wato babu sanatan da a Nigeria ba shi da alfarman nemawa al’umma aiki. Sanin kowa ne babu wata ma’aikata ko hukuma da ta isa ta dauki aiki ba tare da ta bawa sanatoci da yan majalisa ‘slots’ ba. Shikenan da nemawa al’ummarsa gara ya bari gurbin ya tafi wani waje? Jama’a muna fa ganin yadda irin su Sanata Babba Kaita da Barau Jibrin ke ruwan ‘offer’ ga jama’a.
Masu irin halin wannan sanata idan ka duba za ka ga ‘yayansu ne cike fal a NNPC da CBN da NITDA da Maritime da NPA da sauransu. Kuma ba jarrabawa aka yi su ka fi kowa ci ba!
Shi kuma dan talaka da ku ka ki samawa aiki kun fi so in an kada gangar siyasa ya dau gora ko barandami ya kare ku a wajen kamfen. Allah Ya isa!
Jaafar Jaafar
Discussion about this post