Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Aliyu bayyana cewa laifin sa ɗaya ce kawai kuma ita ce kinnkomawa jam’iyyar APC da bai yi ba tare da gwamna Bello Matawalle.
A hira da yayi da BBC Hausa, Mahdi ya ce an maida shi saniyar ware a jihar.
” An maida ni saniyar ware a jihar Zamfara, idan gwamna Matawalle zai yi tafiya baya mika min ragamar mulki sanna. shugabannin tsaron jihar babu mai saurara ta.
” Akwai lokacin da aka samu matsalar harehare a jihar gwamna baya nan. Ko da kira kwamishinan ƴan sanda ƙin ɗaukan waya ta yayi. Ba su ɗaukan waya ta kwatatakwata.
” Haka shima sakataren gwamnatin jiha, idan na kira shi baya ɗaukan waya ta. Sun ɗauke ni ba kowan-kowan ba. Na taba gaya wa gwamna amma har yanzu ba su gyara.
Game da zargin da majalisa ke yi akan mataimakin gwamnan, Mahdi ya ce bita da kulli ne kawai.
” Duk abinda kaga ana yi mini bita da kulli ne kawai. Da ace yau zan koma APC har biki sai an yi min na yi mini maraba. Saboda haka ba laifi na yi ba APC ce dai da ban koma ya sa ake yi min haka.
Mahdi ya ce ba zai bayyana a gaban majalisa ba saboda maganar tuhumarsa da zargi da ake masa duk suna kuto tukunna.