Sanata Ibrahim Shekarau da sauran mambobin kungiyar sa sun zargi kalaman gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje da ingiza ƴaƴan jam’iyyar.
Shekarau ya bayyana cewa uwar jam’iyyar APC ba su yi wa bangaren su adalci ba ganin sune kotu ta fara yanke hukuncin sahihancin zaben su amma ba a basu Danzago shaidar zama shugaban jam’iyyar na Kano ba.
Sai ga shi kotun ɗaukaka kara na yanke hukunci sai uwar jam’iyya ta mika wa Abdullahi Abbas satifiket.
A jawabin da Ganduje yayi bayan nasarar da bangaren sa yayi a kotu ya yi wa bangaren Shekarau laƙabi da ‘Ƴan kungiyar banza bakwai’.
Sai dai kuma kungiyar ta ce lallai zata garzaya kotun koli domin a ganinta ita ce ta yi nasara a zaben da aka yi na jam’iyyar a kan har Kano.
Jim Ƙadan bayan yanke wannan hukunci sai mawaki Rarara ya saki sabuwar waka wacce ya rika yi wa ƴan kungiyar Sanata Shekarau habaici ya cewa sun sha ƙasa.
Dalilin da y sa kotun ɗaukakka kara ta bayyana Abbas shugaban APCn Kano
Kotun daukaka kara ta kwace shugabancin jam’iyyar APC ta Kano daga bangaren sanata Ibrahim Shekarau zuwa bangaren gwaman Abdullahi Ganduje wato karkashin shugabancin Abdullahi Abbas.
Idan ba a mata ba kotu a Abuja ta kwace shugabancin jam’iyyar APC daga hannu bangaren Ganduje zuwa bangaren Sanata Ibrahim Shekarau da ta zabi Haruna Danzago a matsayin shugaban jam’iyyar ta jiha.
Kotun daukaka kara ta ce kotun da ta yanke wancan hukunci bata yi daidai ba domin bata da hurumin ba yanke hukunci ba sauraren karar ma tun daga farko bata ikon yi.
Kotun ta ce doka bata amince akai ga sai an bayyana gaban kuliya ba kafin a warware tarzoma irin haka wanda ta shafi rikicin cikin gida.
A dalikin haka kogtun ta ce jagorancin jam’iyyar APC a jihar Kano dole ya koma ga bangaren su Abdullahi Abbas wanda shine gabadaya ya’yan jam’iyyar a wancan lokaci suka amince shugaban jam’iyyar ba tare da an yi zabe ba.
Matsalar a nan ita ce, ba duga ‘ya’yan jam’iyyar APC ba ne suka amince da wannan zabin su Abbas a matsayin shugabannin jam’iyyar A Kano.
Idan kuma haka ne to ba duka ‘ya’yan jam’iyyar bane kenan suka amince da hakan saba wa dokar jam’iyyar ce.
Yanzu dai akwai yiwuwar sai an garzaya kotun Koli kafin a iya karkare wannan matsala.
Discussion about this post