Gwamna Aminu Waziri Tambuwal dai ya fito tsakiyar fili, ya tuɓe, kuma ya yi shirin kokawa. Idan ma dambacewa za a yi, to Tambuwal ma ya na da ƙwanji da murɗaɗɗen damtsen da duk wanda ya nausa a siyasance, sai ya kai ƙasa.
Idan ka haɗa Tambuwal da wasu dattawan APC da na PDP ɗin su, za a iya kiran sa ‘yaro da gari, abokin tafiyar manya.’
Daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban ƙasa, Tambuwal ne ya fi kowa daɗewa a kan mulki ba tare da ya huta ko an hutar da shi ba.
Ya shiga Majalisar Tarayya cikin 2003, kuma tun daga lokacin bai taɓa faɗuwa zaɓe ba, har ya dangana Shugaban Majalisar Tarayya a 2011.
A shekaru huɗu da ya yi a kan kujerar shugabancin tarayya, babu irin tuggu da gayya da killa da kwatagwangwamar da mulkin Jonathan bai kitsa wa Tambuwal ba.
Bayan ya fita daga APC, Tambuwal ya lashe zaɓen kujerar gwamna karo na biyu a ƙarƙashin PDP a Jihar Sokoto.
Jihohin Kebbi da Sokoto da Zamfara ba su da wani ɗan takarar da ya kai Tambuwal. Domin a zahiri dai babu irin abin da idanun Tambuwal ba su gani ba, a kan batun matsalar tsaro a waɗannan jihohi uku na yankin sa.
Al’ummar waɗannan jihohi za su so a ce sun zaɓi wanda zai warkar masu da wannan azabar matsalar tsaro da ke addabar su. Shi kan sa Tambuwal zai so a ce ya zama shugaban ƙasa domin ya ceto yankin sa daga durƙushewa.
Sai dai kuma zai yi wahala a ce Tambuwal na da guzirin da zai ishe shi wannan doguwar tafiya, a matsayin sa na falken da ya shiga cikin gagga da gogaggun fatake irin su Atiku Abubakar, Bola Tinubu da duk wani falken tafiyar 2013, wanda idan za a shekara dubu ana tafiya a dokar daji, to guzirin su ba ƙarewa zai yi ba.
Tambuwal zai iya samun goyon bayan gwamnoni ‘yan uwan sa. Sai dai kuma tafiyar Tambuwal za ta iya fuskantar matsala, musamman idan gwamnonin PDP na kudancin ƙasar nan suka ce sai ɗan kudancin ƙasar nan zai iya tsayawa takara a zaben 2023.
Daga cikin masu neman takara dai Yahaya Bello na Kogi ne kaɗai ya fi Tambuwal ƙarancin shekaru.
Babu jayayya kuma babu tantama, Tambuwal ya fi Bellon Kogi gogewa da kuma goyayyar siyasa. Kuma ya fi shi buɗe-ido.
Taragon Tambuwal zai iya kai gaci ko da ya na tangal-tangal.
Discussion about this post