Firayi Ministan Birtaniya Boris Johnson ya bayyana tsauraran matakan karya tattalin arziki da ƙasar ta ɗauka a kan Rasha, sakamakon mamaye Ukraniya da Rasha ta yi a ranar Alhamis.
Ya ce Birtaniya tare da amincewar Majalisar ƙasar, ta ƙwace kuɗaɗen manyan bankunan Rasha da ke cikin ƙasar, sannan kuma ta haramta dukiyoyin manyan kamfanonin Rasha da ke ƙasar.
Daga cikin takunkumin akwai kuma haramcin hana manyan kamfanonin Rasha hada-hadar kuɗaɗe, saye ko sayar da kaya a Birtaniya.
An kuma haramta wa duk wani kamfani ko banki na Birtaniya bayar da bashi ga kamfanonin Rasha.
Takunkumin ya shafi wasu manyan kamfanonin Rasha, har da wani kamfani mafi girma da ke shirin ɗaukar ma’aikata miliyan biyu.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Amurka, Tarayyar Turai da G7 su ka ƙaƙaba takunkumi 8 don karya tattalin arzikin Gwamnatin Putin.
Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana cewa Amurka ta ƙwace ilahirin dala tiriliyan 1 mallakin wasu manyan bankunan Rasha 4, waɗanda bankunan ke hada-hada da su a Amurka.
Wannan mataki na ɗaya daga cikin matakan da Amurka ta ɗauka domin ɗanɗana wa Rasha gayyar laifin afka wa Ukraniya da yaƙi da Shugaban Rasha Putin ya yi.
Yayin da Biden ke jawabi a ranar Alhamis, ya ce sun tattauna da Tarayyar Turai wadda ƙungiya ce mai mambobin ƙasashe 27, da kuma mashahuran ƙasashe masu arziki bakwai na duniya, wato G7, su ma duk za su ɗauki matakan ƙwace ilahirin kuɗaɗen bankunan Rasha da ke ƙasashen su.
Biden ya ce za a ɗauki waɗannan tsauraran matakai ne domin a gurgunta tattalin arzikin Rasha, ta yadda al’ummar ƙasar za su ɗanɗana abin da shugaban su ya janyo masu.
Sauran matakan sun haɗa da toshe wasu kafafen hada-hadar kasuwancin Rasha a Amurka da Turai, daina cinikayya da hana Rasha sayar da kayan ta a Amurka da Turai da kuma hana manyan kamfanoni da bankunan ƙasar da manyan ‘yan kasuwar ta yin duk wata hada-hada da neman bashi a Turai da Amurka.
Yayin da Ƙungiyar Ƙasashen Afrika (AU) ta yi tir da mamayar da Rasha ta yi wa Ukraniya, tuni Birtaniya ta bi sahun Amurka, ta ƙaƙaba wa Rasha tsauraran matakai.