Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta ce Dakarun ‘Operation Haɗin Kai’ sun kakkaɓe sama da ‘yan Boko Haram da ISWAP 120 a Arewa maso Gabas, cikin makonni uku.
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya, Bernard Onyeuko ne ya yi wannan ƙarin haske dangane da irin ci gaban da suka samu tsakanin watan Janairu da Fabrairu, a Abuja, a ranar Alhamis.
Ya ce kwamandojin ISWAP masu yawa sun sheƙa barzahu, ciki kuwa har da shugaban su, da su ke kira Amir da wasu sojojin haya daga ƙasashen waje, waɗanda ke haɗa masu nakiya.
Onyeuko ya ce duk an bindige su a hare-haren da aka kai masu ta sama da ta ƙasa.”
Onyeuko ya ce akwai kuma ‘yan ta’adda su 965, tare da iyalan su da suka yi saranda ga Sojojin Najeriya.
Ya ce sun miƙa wuya ne a wurare daban-daban a cikin waɗancan makonni uku.
Ya ƙara da cewa guda 104 da suka yi saranda, sun fito ne daga ɓangaren ISWAP. Akwai kuma mutum 25 da aka ceto daga hannun ISWAP.
Onyeuko ya ce dukkan waɗanda suka yi saranda ɗin an tantance su, kuma an damƙa su ga hukumar da nauyin kula da su ya shafa domin ɗaukar matakan da suka dace na gaba.
Da ya ke bada bayanin nasarar da Sojojin Najeriya su ka samu a Adamawa da Yobe yankin Gorini da ke cikin Ƙaramar Hukumar Gujba a Jihar Yobe, Manjo Janar Onyeuko ya ce “an kashe kwamandojin ISWAP da sauran karabiti da dama.
“A harin farmakin dama ne aka kashe Malam Ari wanda babban kwamandan da ke kula da Kirta Wulgo da wasu sojojin haya ‘yan ƙasashen waje masu haɗa wa ‘yan ta’adda nakiya.
“An kuma fatattake su a Abbaganaram, Bukar Mairam, Chukum Gudu da Jubilaram a Ƙaramar Hukumar Marte.”
Baya ga ‘yan ta”adda da aka kashe su 25, an ƙwace muggan makamai yayin artabun.
Discussion about this post