Jihar Zamfara na neman afkawa cikin ruɗannin siyasa, bayan bala’in kashe-kashe da garkuwa da su ke fama da shi, yayin da Majalisar Jiha ta aika wa Mataimakin Gwamna Mahdi Shehu jerin laifukan shirin tsige shi.
Hakan ya faru ne a ranar Litinin, kwanaki uku bayan da majalisa ta karɓi buƙatar neman tsige Mahdi, wanda ya yi zaman sa a PDP, ya ƙi bin Gwamna Matawalle canja sheƙa daga PDP zuwa APC.
Mataimakin Shugaban Majalisa Musa Bawa ne ya miƙa tulin takardun bayanan da ke ƙunshe da laifuka da buƙatun tsige Mataimakin Gwamna.
Bawa wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin ya nemi a tsige Mahdi daga kujerar sa ta mataimakin gwamna.
Cikin wata sanarwar da Shamsuddeen Basko ya sa wa hannu, wadda kuma an aika ta ga Mataimakin Gwamna ta hannun Sakataren Gwamnatin Jihar Zamfara, takardar ta sanar da Mahdi cewa “mun cika sharuɗɗan da Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya amince, cewa 1/3 na Mambobin Majalisar Jiha sun amince da tsige ka.
“To Majalisa a ƙarƙashin Kakakin Majalisa ta amince da wannan sanarwa kamar yadda doka ta tanadar.”
“Lokacin da muka gayyace ka a cikin 2021, sai ka ƙi zuwa, ka garzaya kotu. Kuma a lokacin ba mu da niyyar tsige ka, kamar yadda aka riƙa yaɗawa.
Ya ce majalisa kuma a lokacin ta bi umarnin da kotu ta bayar.
Cikin laifukan da su ke zargin Mahdi ya aikata, akwai laifin keta alfarmar ofishin sa na Mataimakin Gwamna ta hanyar amfani da ofishin ya azurta kan sa da kuma kasa yin ayyukan sa na ofis a matsayin sa na Mataimakin Gwamna.
Wakilin mu ya kasa samun lambar Kakakin Yaɗa Labarai na Mahdi, mai suna Babangida Zurmi.
Discussion about this post