Shugaba Muhammadu Buhari ya shawarci jam’iyyar sa ta APC cewa su fito da shugaban jam’iyya ta hanyar amincewa da wani ɗan takara ɗaya, ba sai an gwabza zaɓe ba.
Gwamnan Kebbi kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC, Atiku Bagudu ne ya bayyana haka a ganawar sa da manema labarai, bayan gwamnonin sun kallama wani zaman sirri da Buhari.
“Shugaba Buhari ya yi amanna da a samu matsayar cimma amincewa da shugaba, ba sai an yi zaɓe tsakanin ‘yan takara ba. Amma fa ya ce duk wanda ya fito takarar shugabancin kowane ya cancanta. Sai dai abin la’akari, mutum ɗaya ne zai zama shugaba, ko da zaɓen aka yi.
“Fitar da shugaba ta hanyar yarjejeniya na a cikin tsarin dokokin mu. Don haka ya yi kira gare mu cewa mu rungumi tsarin amincewa a fitar da shugaba salum-alum a cikin ‘yan takarar, ba tare da yin zaɓe ba.” Inji Bagudu.
Aƙalla dai mutum takwas ne ke takarar neman kujerar shugabancin APC. Daga cikin su akwai tsoffin sanatoci da masu ci a yanzu, waɗanda wasun su sun shafe watanni su na kamfen.
Bagudu ya ce sun goyi bayan ra’ayin Buhari, domin a baya ma an zaɓe shugaban APC ta tsarin amincewa, ba zaɓe ba.
“Bisi Akande shugaban APC na farko, John Oyegun da Oshiomhole duk ba a yi zaɓe ba, aka amince da su matsayin shugabanni.” Inji Bagudu.
Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai kuwa cewa ya yi a baya an samu rashin fahimta tsakanin gwamnonin, wajen kasa cimma yarjejeniyar ranar da za a yi taron gangami na ƙasa.
Amma yanzu ya ce duk ra’ayin su ya zo ɗaya, an yarda an ɗage taron zuwa ranar 26 Ga Fabrairu, domin a samu damar yin gangamin shiyyoyi, kuma a sasanta rikicin jam’iyya a wasu jihohi da dama. “Duk da dai wasu rigingimun su na kotu.” Inji shi.
Ya kuma ce an amince za a yi karɓa-karɓar muƙamai na shugabannin jam’iyya tsakanin Arewa da Kudu.
“Muƙaman da kudu ta riƙe tsawon shekaru takwas, yanzu Arewa ce za ta riƙe su. Haka su ma Arewa muƙaman da suka riƙe tsawon shekaru takwas, yanzu kudu za su riƙe su.”