Yayin da ya rage shekara ɗaya a yi zaɓuɓɓukan 2023, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi wa sababbin masu zaɓe miliyan 5.8 rajista a aikin da ta ke ci gaba da yi na yi wa masu zaɓe rajista, ya zuwa ranar Litinin, 14 ga Fabrairu.
Hukumar ta faɗa a ranar Litinin cewa mutum miliyan 3.13 daga cikin sababbin da aka yi wa rajistar sun kammala rajistar su baki ɗaya.
Ta ƙara bayanin cewa mutum miliyan 1.3 daga cikin masu rajistar sun yi tasu rajistar ne ta hanyar yanar gizo, yayin da miliyan 1.84 su ka je su ka yi ido da ido.
Ta ce mutum miliyan 1.6 daga cikin masu rajistar maza ne, sannan miliyan 1.5 mata ne, yayin da mutum 27,543 naƙasassu ne.
Hukumar ta kuma ce mutum miliyan 9.9 da su ka yi rajista sun buƙaci a yi masu canjin wurin zaɓe ko a musanya masu katin zaɓen su ko a cike masu bayanan da ke kan katin su.
INEC ta yi la’akari da cewa mutum miliyan 5.2 da su ka bada buƙatar su maza ne, sannan miliyan 4.6 mata ne, yayin da 95,138 naƙasassu ne.
Yawan Masu Rajistar Zaɓe A Nijeriya Sun Haura Na Sauran Ƙasashen Afrika ta Yamma – INEC:
Idan ba a manta ba, Shugaban INEC ta ce yawan masu rajistar zaɓe a Najeriya sun haura yawan na sauran ƙasashen Afrika ta Yamma baki ɗayan su.
A cikin labarin wanda PREMIUM TIMES HAUSA ta buga cikin Disamba, 2022, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfasa Mahmood Yakubu, ya ce yawan masu rajistar jefa ƙuri’a a Nijeriya ya haura yawan masu rajistar jefa ƙuri’a a sauran ƙasashen Afrika guda 14 baki ɗayan su.
Yakubu ya yi wannan bayani ne kwanan baya a lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a Legas.
Ya ce yawan masu jefa ƙuri’a a Nijeriya ya kai mutum 84,004,084, yayin da yawan masu jefa ƙuri’a a sauran ƙasashen Afrika ta Yamma 14 ban da Nijeriya mutum miliyan 73.6 ne.
Ya ce, “Saboda haka yawan masu jefa ƙuri’a a Nijeriya ya haura yawan na sauran ƙasashen Afrika ta Yamma 14 gaba ɗaya da mutum har miliyan 11.
“A yanzu mu na da rumfunan zaɓe 176,846 yawan mazaɓu kuma ya kai 8,809.
“Mun yi namijin ƙoƙarin ganin mun samu ƙarin mazaɓu ne saboda la’akarin da mu ka yi cewa kusan daga 1999 zuwa 2015 ana samun ƙaruwar yawan masu jefa ƙuri’a. Amma zuwa 2021 sun ƙaru sosai har sun kai 84,044,084. Kuma har zuwa 2015 yawan rumfunan zaɓe bai ƙaru ba.
“Dalili kenan na yin ƙoƙarin da mu ka yi na samar da ƙarin rufunan zaɓe 56,873 cikin watan Afrilu, 2021. Yanzu mu na da guda 176, 846 kenan.”
Haka nan ya yi tsokacin cewa ƙarin yawan rumfunan zaɓe ya faru ne saboda yawan masu jefa ƙuri’a da aka ƙara samu sosai. Kuma ya yi mamakin yadda wasu mutane su ka riƙa yi wa wannan ƙarin yawan rumfunan zaɓe mummunar fahimta.
Yakubu ya ce an yi rajistar masu zaɓe 57,908,945 a zaɓen 1999. A zaɓen 2003 kuma an yi wa mutum 60,823,022. Sai kuma mutum 61,567,036 a zaɓen 2007.
A zaɓen 2015 an yi wa mutum 67,422,005. A zaɓen 2019 kuma an yi wa mutum 84,004,084 rajista.
Hakan na nufin yawan masu rajista a Nijeriya za su ƙaru sosai, idan aka haɗa da yawan waɗanda ake ci gaba da yi wa rajista a yanzu.
Discussion about this post