A ranar 3 Ga Fabrairu 1976 Shugaban Mulkin Soja, Janar Murtala Mohammed ya yi sanarwar samar da wani birni mai suna Babban Birnin Tarayya, Abuja. A sanarwar, Murtala ya ce za a gina birnin a tsakiyar Najeriya wanda zai maye gurbin Legas.
Ranar 5 Ga Fabrairu, 1976 kuma aka yi sanarwar kafa Dokar Soja ta 6, wadda ta tabbatar da birnin a dokance.
Yayin da a yanzu Babban Birnin Tarayya, da a gwamnatance ake kira FCT Abuja ya cika shekaru 46 da kafuwa, PREMIUM TIMES ta zauna da Ministan FCT Abuja na 12, Aliyu Modibbo, inda ya baje ta a faifan yadda aka fara ƙirƙirar birnin, aikin ginin ma’aikatu, haɓɓaka da bunƙasar sa da kuma irin ƙalubalen da ya ke fuskanta a yanzu.
Da yake Hausawa na cewa “mai ɗaki shi ya san inda ruwan sama ke zubo masa”, Modibbo wanda ya yi Minista sau uku a Najeriya, kuma shi ne Danburam Gombe, ya kawo hanyoyin da za a magance matsalolin.
Ga Tattaunawar PREMIUM TIMES Da Ministan Abuja Na 12, Aliyu Modibbo
PTH: Ko za ka iya waiwaye da tunanin gaganiyar yadda aka ƙirƙiro Abuja, tunda ga shi yanzu birnin ya cika shekaru 46 da ƙirƙirowa?
MODIBBO: Na ji daɗi da na samu damar ba ku kabarin tarihin kafuwar Abuja, birnin da tun da farko ya ke da ɗarsashi da shauƙi a zuciya ta. Na daɗe da sanin Abuja tun cikin 1982, bayan na dawo daga Amurka.
A wancan lokacin wani ubangida na ne ya ba ni shawara ya ce min tunda ga shi ka dawo kuma ka na da zurfin matakin ilmin Dakta, sannan ga ka matashi, gara ka tafi Abuja ka jaraba sa’ar neman tudun dafawar da ya dace da mai ilmi irin ka. A lokacin kuwa Abuja zan ce maka ƙauye ce kenan.
Ba zan manta ba, tsakanin 1984-1985, babu komai a daidai inda otal ɗin Transcope Hilton ya ke a yanzu, sai rugar Fulani kaɗai. A lokacin ana aikin ginin ɓangaren da ake kira Shehu Shagari Area.
To wancan lokacin ɗaya daga cikin ma’aikatan Hukumar Raya Babban Birnin Tarayya (FCDA), mijin wata ce da na taɓa yin aikin jarida tare da ita a Gidan Talabijin na NTA. Shi ya kawo takardun filaye guda biyu ya ba ni. Ɗaya filin da za a yi gida ne, ɗayan kuma wuri ne da ginin hada-hadar kasuwanci kaɗai aka amince a yi a wurin.
Da farko ma ƙin karɓa na yi, saboda a lokacin Abuja tantagaryar daji ne. Na ce masa wa zai zo cikin wannan surƙuƙin jejin ya zauna?
Amma ga shi a yanzu wannan surƙuƙin daji ya zama birnin da kowa ke tinƙaho da shi. Albarkacin irin jan aiki, kishi da jajircewar da shugabannin mu da suka shuɗe su ka yi. Tun daga tsoffin shugabannin ƙasa zuwa ministocin su har zuwa manyan ma’aikatan gwamnati da masu aikin gine-ginen kwangila. Duk sun sun bada gagarimar gudummawa.
PTH: To ya za ta auna Abuja a yanzu, idan ka yi amfani da sikelin awon farkon hikimar ƙirƙiro birnin da abin da aka cimmawa zuwa yanzu?
MODIBBO: Wato maganar gaskiya na sha faɗa wa mutane duk irin yadda ake sukar ƙasar mu Najeriya ana aibace-aibace, to ya kamata a sani cewa ɗaya daga cikin gagarimi, muhimmi kuma aiki mai albarka da aka samar a ƙasar nan, shi ne ƙirƙira da gina Abuja. Domin ka ma kalli dukkan biranen Afirka da wasu wuraren. Ka kalli Abuja a yanzu, idan ka haɗa ta da wasu biranen da suka haura shekaru 100 zuwa 200 da kafuwa, za ka yarda cewa Najeriya ta shiga gaban su. Kuma idan ka bincika a intanet za ka ga Abuja na ɗaya daga cikin birane biyar mashahurai ko fitattu na Afrika, waɗanda sauran duk sun ma girmi Abuja da shekaru 100 zuwa 200 da kafuwa.
Saboda haka ba ƙaramin ci gaba ba ne a ce ƙasa ta gina ko ta kafa ƙasaitaccen birni kamar Abuja a cikin shekaru 46 kaɗai zuwa yanzu.
Kuma idan kun tuna, ai a lokacin da Kwamitin Akinola Aguda wanda ya zaɓi Yankin Abuja ya zama Babban Birnin Tarayya, tantangaryar surƙuƙin daji ne a lokacin, babu komai sai ‘yan bukkokin tsirarun jama’a daban-daban. Don haka siyasa ce da wasu dalilai har wasu su fito su na iƙirarin su ne ‘yan asalin yankin.
Yankin Abuja na kowa ne, shi ya sa kowa ya riƙa zuwa ana bada filaye suna ginawa har birnin ya cika, ya bunƙasa zuwa yadda ya ke a yanzu.
PTH: A matsayin ka na Tsohon Ministan FCT Abuja me za ka iya tunawa muhimman abubuwa yanzu a tarihance kan yadda mafarkin gina Abuja ya zama gaskiya?
MODIBBO: To ka san an fara kiki-kaka. Amma da ya ke Tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari ya kasance mai shauƙin ganin mafarkin kafa Abuja ya zama gaskiya, ya yi ƙoƙari sosai. Sannan kuma ya ɗora mutane nagartattu a wurin aikin. Sai da kuma a lokacin babu bayyanar fasaha da fikirar wayewa kamar yanzu.
Dalili kenan idan ka je wasu wuraren ka ga titinan da aka yi, a yanzu mamaki za ka yi ka ce ‘wa ya gina wannan titin haka?’ Amma kuma a lokacin su ne mafi ƙayatarwa.
Shagari ya yi ƙoƙarin da har bukin murnar samun ‘yanci ya yi a Abuja, na Ranar 1 Ga Oktoba, 1981. Shi ya gina Aguda House, har ya ɗan zauna ciki a matsayin Fadar Shugaban Ƙasa a lokacin. Yanzu a can ne Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya ke.
Yadda Buhari Ya Dakatar Da Aikin Gina Abuja A 1983 -Aliyu Modibbo:
Ba zan manta ba, lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari na yanzu ya zama shugaban mulkin soja cikin 1983, sai ya yi biris da aikin gina Abuja gaba ɗaya, har kusan shekaru biyu. Aka daina gini gaba ɗaya, a lokacin Janar Mamman Batsa ne Ministan Abuja.
Amma ayyukan gina Abuja gadan-gadan kuma gabagaɗi sun fara ne a lokacin Shugaba Ibrahim Babangida, a ƙarƙashin Ministan FCT Abuja na lokacin, Manjo Janar Hamza Abdullahi.
Mu da muka samu damar riƙe muƙamin Minista a Abuja mun san cewa lokacin da aka fi samun ‘fatahin’ yin gagarimin ayyukan gina Abuja, shi ne zamanin Mainistan Abuja Hamza Abdullahi. Saboda ya tashi tsaye wajen kawo ‘yan kwangila nagartattu waɗanda suka iya aiki, ga kuma kayan aikin.
Dukkan mu, har El-Rufai zai shaida maku cewa mutumin da ya aza harsashen Abujar mu ta yanzu shi ne Hamza Abdullahi.
To daga nan kuma sauran Ministoci da muka biyo bayan sa, sai muka ci gaba da ɗorawa daga inda ya tsaya. Saboda aikin gina Abuja tsari ne a dokance wanda babu mai iya kauce masa. Duk abin da ka ga ana bi a Abuja, tsari ne dama wanda tun fil azal ya na nan a zayyane. Duk titin da aka an gina ko ana kan gini a yanzu, ko za a gina nan gaba, ba wani sabon abu ba ne wani ƙirƙiro. Dama can akwai shi a taswirar gina Abuja. Haka waɗanda suka tsara taswirar birnin suka zayyana shi. Kuma ba mai kaucewa ko karkacewa ko waskewa a kan hakan.
Mun gode Allah, saboda yankin FCT Abuja ba kamar Legas ba ne, shi ya sa mu ke iya tsara shi fiye da Legas ba ne. Saboda su can akwai sarautar gargajiya. Nan kuwa fili ne ga shi nan ya nausa a cikin daji, kuma babu tsadar biyan diyya filaye ko gine-gine ko ƙasa kamar Legas.
Yadda Na Samar Da Tsatsauran Tsaro A Abuja – Aliyu Modibbo:
Kun san kowane Ministan Abuja da irin na sa salon mulkin. Ni a nawa taƙaitaccen lokacin, na fi maida hankali ne wajen samar da tsaro. Saboda ina so birnin Abuja da yankin gundumar baki ɗaya a samar da tsaro ga jama’ar da ke cikin sa. Kuma hakan na yi bakin ƙoƙari na sosai. Kuma zan iya bugun ƙirjin cewa mun rage aikata muggan laifuka matuƙar gaske a lokacin. Daga nan ne kuma sai na koma kan sauran fannonin inganta zayuwar jama’a.
PTH: To mene ne babban ƙalubale?
MODIBBO: Mun gode Allah, ga shi har mun cika shekaru 46. Amma fa dukkan waɗannan nasarori su na tare da ƙalubale, kuma idan ba a yi da gaske ba, to za su yi wahalar magancewa ko kawarwa.
Wannan babban ƙalubale kuwa shi ne yawan ɓarkowar da mutane ke yi a cikin birnin. Domin ya cika ya batse, fiye da yadda aka tsara yadda zai kasance, nesa ba kusa ba.
Idan ka dubi Abuja Sashe Na 1 – Wuse 1, Wuse 2, Garki, Maitama, Asokoro, Central Area. Da kuma Abuja Sashe Na 2, Utako, Guzape, Wuse, Jahi, sai Sashe Na 3 shi ne wanda El-Rufai ya fara, wato garuruwan gefen Birnin Tarayya, irin su Karmo, Jikwoyi, Nyanya, kai har ka dangana cikin Jihar Nassarawa irin su Mararaba, Masaka, duk cike su ke danƙam da ɗimbin mutane.
Za ka tsallaka Nyanya ka shiga Jihar Nassarawa. To yawan jama’a da ke cikin Abuja ne ke tilasta mutane zuwa su zauna waɗancan garuruwa da ke gefen birnin. Za ka ga mutane daga nan har Keffi, amma yawanci a cikin Abuja su ke zuwa kullum su yi harkokin su, su koma gidajen su.
Sannan idan ka duba za ka ga a ɓangaren Zuba da Madalla inda muka yi iyaka da Neja da Kaduna, an ƙure wurin babu filaye.
Inda ake da wadatar filaye yanzu shi ne ɓangaren da idan ka nausa ka yi iyaka da Kogin Neja, Kogi da Gwagwalada, Abaji duk akwai filaye. To daga inda aka ce maka daga irin su Lokogoma har zuwa Abaji sun cike da yawan jama’a, za ka taras kenan an samu wajen mutum miliyan uku a yankin FCT Abuja.
Ba zan manta ba, yadda aka tsara Abuja, ba a so mutanen da ke cikin Wuse, Garki, Maitama da Asokoro su wuce mutum 500,000.
Amma a yanzu ina tabbatar maka duk wanda ya shigo Abuja ba ya son fita. Saboda lokacin da ina Minista, na sa an yi min wannan binciken. Muka kafa na’urar da ke ƙididdige motocin da ke shigowa a kullum da kuma waɗanda ke fita.
Sai muka gano cewa aƙalla rabin motocin da ke shigowa, ba su fita. Wannan da ina faɗa maka mun yi ƙididdigar tun cikin 2007. To ina tabbatar maka yanzu idan za’a yi irin wannan ƙididdigar, za a samu mutanen da idan sun shigo ba su fita sun nunka yawan waɗanda ba su fita a 2007 sau uku ko ma sau huɗu.
Mutane ba su son fita Abuja idan sun shigo, saboda an tsara birnin ya kasance shi kaɗai ne birni mai tsarin gina garuruwa bisa tsawira ingantacciya mai tafiya da zamani. Don yanzu idan ka kula, a cikin birnin Abuja dai babu inda za ka je ka ji wari ya dame ka a cikin unguwar. Sai fa a garuruwan da ke kewaye da Abuja.
A irin su Kano da Legas da Benin da Fatakwal, duk ginin masai za ka gani a ban-ɗakunan su. Shi ya sa wari ke fitowa ya na damun mutane. Amma a cikin Abuja ba a gina ramin masai domin bahaya a ban-ɗakuna. Komai a ƙarƙashin ƙasa ya ke, wato tsarin bai-ɗaya na ‘sewer’, wanda kuma shi ya fi dacewa da biranen Afirka.