Masu nazarin siyasa da masu jefa ƙuri’a baki ɗaya, sun yi tunanin jam’iyyar APC za ta kame kan ta daga irin zubar da kima da mutuncin da PDP ta yi, har ta rasa mulki bayan shafe shekaru 16 a jere.
Rigingimu su keta PDP cikin 2006 da kuma 2014, waɗanda su ka ja mata asarar mulki, lamarin da har yau APC ba ta daina yi mata bi-ta-da-ƙulli ba, tun bayan faɗuwa zaɓe cikin 2015.
Shekaru bakwai ɗin da PDP ta yi zuwa yau ta kasa kimtsa kan ta. Daga yau ta yi wawan-zama a tsakiyar kasuwa kowa na kallon al’aurar ta, gobe kuma sai ta ɗibga tulin abin kunya, ta yi sata gidan surukan ta. Ki kuma ka ga dangin uwar APC sun kaure faɗa tsakanin su da dangin uba.
APC wadda auren gamin-gambizar ACN, CPC, ANPP da APGA ne suka haife ta, shugaban ta na farko shi ne Bisi Akande.
Tun a ranar 6 Ga Fabrairu, 2013 aka fara batun yin gambiza, amma sai bayan wata biyar aka yi mata rajista, a ranar 31 Ga Yuli, ,2013. Daga nan ta yi mulki a 2015 , sannan ta sake lashe zaɓe a 2019.
Shekaru 9 bayan kafa APC, wannan jam’iyya mai mulkin ƙasa mai yawan al’umma miliyan 200, ta shiga rikici, ta afka cikin gararin da ke neman gagarar ta sasantawa.
Tun bayan sauke Adams Oshiomhole daga shugabanci APC ba ta sake zama lafiya ba. Dama kuma cutar amai da gudawar da jam’iyyar ta yi fama da shi ne a ƙarƙashin shugabancin Oshiomhole ya sa aka cire shi.
An naɗa Shugabannin Kwamitin Riƙo na Mutum 13, a ranar 25 Ga Yuni, ƙarƙashin Gwamna Mala Buni na Jihar Yobe. Aka ɗora masa alhakin shirya taron gangami ƙasa, cikin watanni shida. Amma har yanzu fiye da shekara ɗaya kenan, Buni ya kasa gudanar da taron gangami.
Hakan ya sa gwamnonin APC yin taro a cikin Nuwamba, 2021 a Abuja suka aza rana cewa za a yi gangami a cikin Fabrairu, 2022.
Hasalallun ‘Yan APC Sun Maka Jam’iyya Kotu, Su Na Ƙalubalantar Gangamin Fabrairu Da Shugabancin Mala Buni:
Tunanin da jam’iyyar APC ke yi na shirya gangamin taron ƙasa na neman samun cikas, yayin da wasu mambobin jam’iyya da aka ɓata wa rai sun maka uwar jam’iyya kotu, domin buƙatar a dakatar da taron.
Wata ƙarar kuma wadda wani hasalallen ɗan jam’iyya ya shigar, shi kuma ya nemi kotu ta gaggauta tsige Gwamnan Yobe Mai Mala Buni daga shugabancin jam’iyya na riƙon-ƙwarya.
Mutanen biyu duk sun shigar da ƙarar ce a Babbar Kotun Tarayya, Abuja, tsakanin watan Disamba 2021 zuwa Janairu 2022.
A ƙarar neman hana shirya taron wadda gungun wasu mutane biyar suka shigar, sun maka Mala Buni ne a kotu, tare da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC.
Hasalallun da su ka shigar da ƙara sun haɗa da Suleiman Usman, Mohammed Shehu, Samaila Isahaƙa, Idris Isah da Audu Emmanuel.
Ƙarar wadda aka shigar a ranar 4 Ga Janairu, sun nemi kotu ta dakatar da gangamin taron ƙasa da ake shirin yi a cikin Fabrairu.
Tuni gwamnonin APC sun shirya taro tsakanin Asabar da Lahadi, a Gidan Gwamnatin Jihar Kebbi, a Abuja.
Dama an daɗe ana neman a canja ranar shirya taron.
Cikin ƙara mai lamba FHC/ABJ/CS/3/2022, masu shigar da ƙara ta hannun lauyan su sun shaida wa kotu cewa su na so a dakatar da taron kuma kada a zaben shugabannin jam’iyya na ƙasa, saboda ba a kammala ko ba a yi zaɓen fidda gwani a wasu jihohi ba.
Sun nemi kada APC ta shirya zaɓen shugabannin jam’iyya a ranar gangami har sai ta fara shirya zaɓen wasu jihohi da da suka haɗa da Anambra da Zamfara tukunna.
Kuma sun nemi kotu ta hana INEC bayar da izni APC ta yi zaɓen shugabanni na ƙasa, ba tare da an yi na sauran jihohin da ba a yi ba.
Shugaban Matasan APC Ya Maka Mala Buni Da INEC Kotu:
Shugaban Matasan APC na Ƙasa, Zahraddeen Audu ya maka Mala Buni kotu, inda ya ƙalubalanci shugabancin sa a cikin APC.
Ya nemi kotu ta umarci Buni ya daina kiran kan sa shugaban jam’iyyar APC na Riƙo.
Ya shigar da ƙara a ranar 10 Ga Disamba, 2021, inda ya ce a matsayin Mala Buni na Gwamnan Jihar Yobe, tsarin mulki ya hana shi riƙe wani muƙami daban.
Gargaɗin Minista Keyamo: Mala Buni Haramtaccen Shugaban Jam’iyya Ne:
Farkon watan Satumba ne Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo ya yi kakkausan gargaɗin cewa mulki zai iya suɓucewa daga hannun APC, idan Gwamna Buni ya ci gaba da shugabancin jam’iyyar ko na tsawon sati ɗaya ne.
Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo, ya gargaɗi jam’iyyar APC cewa akwai gagarimar matsalar da ta tunkari jam’iyyar, matsawar Gwamna Mai Mala-Buni na Jihar Yobe ya ci gaba da kasancewa Shugaban Jam’iyya na Riƙo har zuwa jibi Asabar, ranar zaɓe shugabannin APC a matakan Kananan Hukumomi da Jihohi da za’a yi ranar 31 Ga Yuli.
Yayin da ya aika da wata wasiƙar gaggawa ga jam’iyya s asirce, wadda ta faɗo hannun PREMIUM TIMES, Keyamo wanda shi ma gogaggen lauya ne, ya bayyana haramcin riƙe APC da Gwamna Buni ke yi, domin Dokar Ƙasa da Dokar APC sun haramta Gwamna ya riƙe wani muƙami ko shugabanci banda na gwamna da aka rantsar da shi don ya riƙe.
Wannan mahaukaciyar guguwa ta taso ne sanadiyyar hukuncin da Kotun Ƙoli ta Yanke, inda ta jaddada nasarar Gwamna Rotimi Akeredolu na Ondo, na APC, kan Eyitayo Jegede na PDP.
Yadda Sakacin Lauyoyin Jegede Ya Bai Wa Akeredolu Nasara A Ɓagas:
Keyamo ya ce Jegede ɗan takarar PDP ya shigar da Gwamna Akeredolu ƙara, bisa zargin zaɓen da bai cancanta ba, domin a lokacin da aka yi zaɓen cikin Oktoba 2020, Gwamna Mala Buni ne Shugaban Riƙon APC, wanda haramun ne a Dokar Ƙasa Sashe na 183 na 1999 Gwamna ya riƙe wani muƙami daban da na Gwamna.
Haka ma Dokar APC Sashe na 17 ya haramta wa Gwamna riƙe wani muƙami lokacin da ya ke kan mulki.
“Inda Jegede da lauyoyin sa su ka kwafsa shi ne da ba su haɗa da sunan Gwamna Mala Buni Shugaban Riƙon APC tare da na Gwamna Rotimi sun maka su kotu tare ba.
“Da an haɗa da sunan Shugaban Riƙon APC, to da a ranar Litinin Kotun Koli ta soke zaɓen ta bai wa Jegede na PDP nasara.” Inji Keyamo.
A kan haka ne Keyamo ya bada shawarar cewa lallai kamata ya yi a ɗage zaɓen shugabannin APC na Ƙananan Hukumomi da na Jihohi da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar mai zuwa.
“Domin banda Mai Mala-Buni, akwai Gwamnonin Osun da na Neja a cikin Kwamitin Amintattun APC, waɗanda su ma bai kamata a saka su a ciki ba.
Ya ce idan aka yi zaɓen shugabannin jam’iyya a ƙarƙashin Buni, to duk wanda ya ci zaɓe a ƙarƙashin APC, tun daga kan kansila har shugaban ƙasa sai kotu ta ƙwace kujerar sa.
A kan haka ne ya bada shawara a ɗage zaɓe na shugabannin ƙananan hukumomi da na Jihohi. Sannan a gaggauta cire Mala Buni, ta hanyar taron Majalisar Zartaswar APC na gaggawa, wanda zai cire waɗannan shugabannin riƙo, ya naɗa wasu.
Gwamna Rotimi ya tsallake rijiya ne saboda Alƙalai huɗu daga cikin bakwai ne su ka yarda da zaɓen sa bisa dalilin cewa sun yarda Gwamna Buni bai cancanci riƙe jam’iyya ba, amma mai ƙara fa bai shigar da Buni a cikin ƙarar da ya shigar ba.
Sauran lauyoyi uku kuwa su ka ce ba sai an sha wahalar shigar da sunan Buni ba, tunda dai bai cancanci shugabancin APC ba, to Gwamna Rotimi bai ci zaɓe ba ƙarƙashin APC kenan.
A kan haka ne Keyamo ya ce wannan shari’a ta nuna kenan duk wanda zai kai ƙarar APC nan gaba, to matsawar ya haɗa da sunan Buni, ko tantama babu nasara zai yi a kotu.
Taron Gangamin Da APC Za Ta Yi A Ranar 26 Ga Fabrairu, 2022:
Yanzu dai ta tabbata APC za ta yi gangami a ranar 26 Ga Fabrairu, a Abuja. Mala Buni da Shugaban Gwamnonin APC Kayode Fayemi duk sun tabbatar da haka. Sai dai kuma tabbas akwai rikici, domin ko a kwanan nan sai da Babban Daraktan Ƙungiyar Gwamnonin APC ya ajiye aiki, bisa abin da ya kira sakin hanya madaidaiciya da APC ta yi.
Baya ga irin su Minista Keyamo masu nuna haramcin shugabanincin Buni da irin illar da zai haifar wa APC nan gaba a kotu, ita ma jam’iyyar PDP ta nemi a tsige shi, ta ce haramtacce ne.
Akwai masu raɗe-raɗin cewa Buni ya maƙale kan kujerar APC don ya ci gaba da yaɗa manufofin sa na neman zama mataimakin shugaban ƙasa, idan aka miƙa takarar mataimaki ga yankin Arewa maso Gabas.
Shi kuma Sakataren APC John Akpanudoedehe an ce ya maƙale ne saboda ya na son tsayawa takarar gwamna a jihar sa Akwa Ibom.
Rigingimun APC A Jihohi 16:
Yayin da gangamin watan Fabrairu ya ƙarato, a lokacin kuma APC na fama da rikicin shugabanci na jiha a jihohi 16 da suka haɗa da Zamfara, Kano, Abia, Kwara, Osun, Delta da Cross Riba. Sai kuma Ogun, Oyo, Akwa Ibom, Kebbi, Ribas, Legas, Enugu, Imo da Ekiti.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labaran ƙaƙudubar rikicin APC a Kano, inda shugabancin jam’iyya ya suɓuce daga hannun su Gwamna Abdullahi Ganduje. Ta kuma sha buga rikicin jihar Kwara, inda inda Gwamna da Ministan Yaɗa Labarai Lai Mohammed suka keta fatarin APC gida biyu, kowa ya keci tsagi ɗaya.
Rikicin baya-bayan nan shi ne na Jihar Kebbi, inda APC ta rikice daga sama har ƙasa, saboda zargin ƙoƙarin da Gwamna Abubakar Bagudu ke yi don ya ɗora Ministan Shari’a Abubakar Malami ya zama ‘halifan sa.’
Wannan ya haifar da rikici tsakanin Sanatocin APC, su Adamu Aliero da kuma Gwamna Bagudu.
A Jihar Gombe, sai dai a ce har yanzu ta-ciki na ciki, tsakanin ɓangaren Gwamna Inuwa Yahaya da ɓangaren Sanata Ɗanjuma Goje.
Duk da an shirya bayan yaƙin da ya haddasa asarar rayuka a tsakanin su, ana ganin har yau akwai sauran rina a kaba.
Da alama dai Kwamitin Sasantawar da jagoran APC Bola Tinubu ya jagoranta cikin 2018, har aka samu aka sake lashe zaɓen 2019 ko dai akwai sauran aiki a gaban sa, ko kuma akwai buƙatar sake kafa wani irin sa, domin ya kashe wutar da ke cin tulin tsintsiyar APC.
Saboda matsawar wutar ta ci gaba da ci, to APC za ta iya rasa tsintsiyar da za ta share masallaci, kasuwa ko tasha.