A ci gaba da bayyana Sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da ake yi a babban birnin tarayyar Najeriya ranar Asabar, jam’iyyar PDP ta lallasa jam’iyyar APC a karamar hukumar Bwari.
Malamin zaɓen Amochi Madu, a lokacin da yake bayyana sakamakon zaben ya ce John Gabaya na jam’iyyar PDP ne yayi nasara a zaben shugaban karamar hukumar Bwari.
A cewar sa Gabaya ya samu kuri’u 13,045 inda shi kuma Audi Shekwolo na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 7,697.
Abubakar Abdullahi na jam’iyyar APGA ne ya zo na uku da kuri’u 600 kacal.
Gundumar Gwagwalada
Ɗan takaran jam’iyyar APC na karamar hukumar Gwagwalada Jubrin Abubakar ne ya lashe zaɓen kujerar shugaban karamar hukumar Gwagwalada a zaɓen ranar Asabar.
Jubrin ya doke Muhammed Kassim na jam’iyyar PDP da kuri’u 11,121 inda Kassim na PDP ya samu kuri’u 9000 da ƴan kai.
Tuni dai malamin zaɓe ID Umar ya bayyana, Jubrin wanda yayi nasara a zaben.
AMAC
A gundumar AMAC kuma jam’iyyar APC ce ta sha kashi a hannu jam’iyyar PDP a bayanan sakamakon zaɓen da aka faɗi ranar Lahadi.
Christopher Zakka (Maikalangu) na jam’iyyar PDP ya yi nasara a kan abokin takarar sa na jam’iyyar APC Murtala Karshi (Yamarayi).
Zakka ya sami kuri’u 19,302 inda shi kuma Karshi ya samu kuri’u 13,249.
Kuje
A karamar hukumar Kuje, Suleiman Sabo na jam’iyyar PDP ne yayi nasara a zaben shugaban karamar hukumar Kuje.
Sabo ya doke Sarki Hamidu na jam’iyyar APC da kuri’u sama da 6000.
Sabo ya samu kuri’u 13,301, shi kuma Sarki na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 7,694.