Aƙalla ƙananan yara ‘yan ƙasa da shekaru 5 har su miliyan 1.4 ne za su yi fama da ƙarancin abinci mai gina jiki a cikin shekarun da ake tunkara a yanzu.
Wannan matsala kuwa na shirin afkuwa ne sakamakon yaƙe-yaƙen ta’addanci da Boko Haram ke yi a Arewa maso Gabas.
Ofishin Kula da Ayyukan Agaji da Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya (UN-OCHA) ne ya bayyana haka.
Kodinetan Ayyukan Agaji da Jinƙai na Majalisar Ɗinkin Duniya a Najeriya, Matthias Schmale ne ya bayyana haka a Abuja, a lokacin da ya ke miƙa Rahoton Tsare-tsaren Ayyukan Jinƙai da Agaji na 2022 da ƙungiyar su za ta sa a gaba.
“Wannan kirdado da muka yi abin damuwa ne sosai, domin lamarin ya na da ban-tsoro matuƙa.”
Ya ci gaba da cewa, “domin tuni matsalar yunwa ta fara cin ƙarfin jikin miliyoyin yara ƙanana a yankin Arewa maso Gabas na Jihohin Adamawa, Barno da Yobe.
“Ni a yanzu ma tsoron da na ke ji shi ne abin da zai faru a wannan kaka ko damina mai zuwa na rashin abinci mai gina jiki ga ƙananan yara. Saboda tuni ana ta kai yara marasa ƙarfin kuzarin abinci mai gina jiki a Cibiyoyin Kula da Yara Masu Rashin Abinci Mai Gina Jiki. Kuma abin sai ƙara ta’azzara ya ke yi, saboda yawan yaran da ake kaiwa cibiyoyin a kullum, tun daga 2017.”
“Na ziyarci wata Cibiyar Kula da Yara Marasa Abinci Mai Gina Jiki da ke Bama Jihar Barno cikin watan jiya. Hankali na ya tashi da na ga cibiyar ta cika danƙam da yara marasa lafiya fiye da adadin da ya makama cibiyar ta iya ɗauka.
“A irin abin da na gani, cikin wannan shekara za a iya samun ƙarin yawan ƙananan yara masu fama da ƙarancin abinci mai gina jiki har miliyan 1.4.”
Yayin da Schmale ya jaddada ci gaba da tallafa wa Gwamnatin Najeriya wajen ganin an agaza wa mabuƙata marasa galihu, ya kuma yi alƙawarin cewa ƙungiyar su za ta gudanar da ayyukan agaji da jinƙai har na dala biliyan 1.1 ga al’umma sama da miliyan 5.5 mabuƙata cikin 2022.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce za a kashe waɗannan maƙudan kuɗaɗen a fannin samar wa yara miliyan 3 abinci mai gina jiki na dala miliyan 144.28, sai dala miliyan 52.68 wajen inganta harkokin lafiya ga mutum miliyan 4.9.
UN za ta kashe dala miliyan 83.17 wajen bunƙasa harkokin ilmin mutum miliyan 1.87 sai kuma dala miliyan 56.80 wajen samar da muhalli ga mutum miliyan 2.95 marasa galihu.