Kakakin rundunar ƴan sandan Kaduna Mohammed Jalige ya tabbatar da fashewar bam a unguwar Kabala West dake cikin garin Kaduna.
Jalige ya shauda wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya NAN cewa babu wanda ya rasa ransa ko kuma rauni a fashewar bam din.
” Babu wanda ya ji rauni ko kuma rasa rai. A lokacin da bam din ya fashe babu kowa a gidan. Zuwa yanzu mun tattara sauran abin da ya fashe din kwararru na dubawa domin sanin ainihin abinda ya fashe.
Jalige ya ce rundunar zata bada karin bayani nan gaba.