Kotun gargajiya dake Igando a jihar Legas ta raba auren Adeola Ajatoye saboda korafin da ya ke yi akan matan sa na yawan roko da hada da take dashi.
“Dole kotu ta yi amfani da hujojjin da Ajatoye ya gabatar ba tare da ta ji daga wajen Chottia ba saboda taki ta amsa gayyatar kotun.
“Kotu ta so ta sassanta ma’auratan ko dan saboda ‘yarsu guda daya da suka haifa tare amma rashin amsa gayyatan da Chottia ta ki yi ya sa dole ayi amfani.
Adeniyi ya raba auren sannan ya bai wa Ajatoye iko kula da ‘yarsu.
Ya ce Chottia ta yi gaggawan kwashe na-ta-ina ta ta daga gidan Ajatoye domin babu aure a tsakanin su