Sanata Ibrahim Shekarau ya gindaya cewa APC ɓangaren sa ba zai amince da kwamitin shugabannin jihar da ba bisa adalci aka zaɓo su ta hanyar yin raba-daidai ba.
Ya ce ɓangaren sa ba zai amince da ɗauki-ɗora, ƙarfa-ƙarfa ko maida wani ɓangare saniyar-ware ba.
Wannan sharuɗɗa na cikin waɗanda wata sanarwa da mutum bakwai suka sa wa hannu kuma suka raba wa manema labarai a ranar Lahadi da dare.
Idan ba a manta ba dai uwar jam’iyya ta ƙasa ta gana da ɓangaren Shekarau da na Ganduje a ranar Asabar, inda aka amince cewa ɓangarorin biyu za su raba muƙamai.
Uwar jam’iyya ta ce za ta fito da tsarin yadda ɓangarorin biyu za su raba muƙamai, da kuma yadda za a tabbatar da cewa an bi ƙa’idar da aka gindaya.
Cikin sanarwar da ɓangaren Shekarau ya fitar ɗin a ranar Lahadi, ta yi kira ga mambobin jam’iyyar APC su kwantar da hankalin su tare da kasancewa masu biyayya ga jam’iyya, har zuwa lokacin da tsarin sasantawar da aka ɗauko ya kawo ƙarshe.
Waɗanda suka sa hannu a kan takardar sun haɗa da Sanata Ibrahim Shekarau na Kano ta Tsakiya, Sanata Barau Jibrin na Kano ta Arewa, Mamba Tijjani Joɓe na Rimingado/Tofa, Nasiru Gabasawa na Gabasawa da Gezawa, Haruna Dederi na Ƙaraye da Rogo, Sha’aban Sharaɗa na Birnin Kano da Shehu Ɗalhatu, Shugaban Buhari Support Group.
Sai dai kuma duk da wannan takarda da su ka fitar, sun ce har yanzu ba su yanke hukuncin matsayar da suka ɗauka ba tukunna.
Discussion about this post