Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) Reshen Jihar Legas, ta yi kira ga ‘yan Najeriya su tunkari gwamnatin tarayya gar-da-gar a kan matsalar da ke damun jami’o’in gwamnati, waɗanda su ke tilasta tafiya yajin aiki.
ASUU ta ce ƙungiyar na tafiya yajin aiki ne sai bayan ta yi iyakar dukkan ƙoƙarin sadantawa, amma abin ya faskara.
Idan ba a manta ba, ASUU ta nemi mambobin ta su ware rana ɗaya domin wayar wa ‘yan Najeriya kai cewa su na ja-in-ja da gwamnati ne domin su ceto jami’o’in ƙasar nan daga durƙushewa.
ASUU ta ce har yau Gwamnatin Buhari ta ƙi cika alƙawarin da ta ɗauka cikin 2020, wanda ɗaukar alƙawarin ne ya sa ASUU ta janye yajin aikin da ya shafe watanni 9 su na yi.
A jawabin sa yayin taron ganawa da manema labarai a Jami’ar Legas da ke Akoka, a ranar Talata, Shugaban ASUU na Legas, Adelaja Odukoya, ya ce rashin cika alƙawarin da gwamnatin Buhari ta yi lokacin da ta lallashe su har suka janye yajin aikin watanni 9 cikin 2020, shi ne zai sake haddasa masu tafiya wani yajin aikin.
“Don haka a tuhumi Gwamnatin Tarayya, laifin ta ne na rashin cika alƙawari idan mu ka sake tafiya wani yajin aiki, wanda babu makawa sai mun tafi nan gaba kaɗan, kwanan nan.” Inji shi.
Cikin makon jiya ne Buhari da shugabannin addinai sun yi wa malaman jami’a magiya kada su tafi yajin aiki.
Shugaba Muhammadu Buhari ya roƙi Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Kasa (ASUU) cewa Gwamnatin Tarayya za ta cika alƙawurran da ta ɗaukar masu, amma su yi wa Allah su yi wa Annabi kada su tafi yajin aiki.
Ya ce yajin aikin zai dagula zangon karatun ɗalibai. Buhari ya ce gwamnatin sa za ta ƙara danƙara maƙudan kuɗaɗe domin inganta tsarin ilmi.
Buhari ya yi wannan alƙawari a lokacin da ya karɓi baƙunci Ƙungiyar Shugabannin Addinai, a ƙarƙashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar da Shugaban Ƙungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN), Samson Ayekunle.
A ranar Juma’a ce dai ASUU ta zargi Gwamnatin Tarayya da cewa ba ta iya cika alƙawurran da ta ke ɗauka a baya, wa. Kan haka ne ASUU ta ce gwamnatin tarayya ta ƙware wajen iya faɗa-ba-cikawa.
Amma kuma da Buhari ke magana, ya ce duk al’ummar da ke fatan ci gaba da kuma alheri, ba za ta yi wasa da harkokin ilmi ba.
Daga nan Buhari ya jinjina wa ƙungiyar mai lakabi da NIREC kan shiga tsakanin da ta yi wajen kawo ƙarshen yajin aikin da ASUU suka shafe shekara ɗaya su na yi.
Kafin nan dai sai da Buhari ya karɓi baƙuncin Kwamitin 2022 Na Musamman Na Manyan ‘Yan Kasuwa, Siyasa, Kafafen Yaɗa Labarai da Shugabannin Kungiyoyin Sa-kai da Kare Haƙƙoƙi, inda ya shirya masu walimar cin abinci tare da shi.
A wurin walimar ce Buhari ya shaida masu cewa Gwamnatin 2023 za ta gaji ingantacciyar dimokraɗiyya da ƙarfafan hukumomin tsaro.
Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa gwamnatin 2023 wadda za ta gaje shi, za ta gaji tattalin arzikin ƙasar da aka bunƙasa ta hanyar inganta harkokin noma a cikin ƙasa, ingantacciyar dimokraɗiyya da ƙarfafan hukumomin tsaron da aka farfaɗo da su.