Duk da matsalar tattalin arziki da mumnunan halin rashin tsaron da ya kassara miliyoyin jama’a, Gwamnonin Najeriya sun fara haƙilon ganin an ruɓanya harajin da ake karɓa a cikin ƙasa har kashi 200%, wato nunki biyu.
Nunki biyu na nufin wanda ke biyan Naira 15,00 a misali, zo zai riƙa biyan Naira 45,000 kenan.
Gwamnonin sun fara wannan shiri ne tare da haɗa baki da Hukumar Kula da Harajin Bai-ɗaya, wato Joint Tax Board.
Sun fito da wani tsarin rariyar manhaja da suka sa wa suna Data for Tax, ko D4T a taƙaice.
Tsari ne da za a tattara bayanan irin sana’a, yayanin samu da yawan kuɗaɗen shigar da ɗaiɗaikun mutane kowane ke samu da na kamfanoni da masana’antu.
“Za a riƙa killacewa tare da taskance dukkan wata hada-hadar kuɗaɗen da mutum shi ɗaya tilo ya yi, ko kuma wanda kamfani ko masana’anta ya yi.
“Za riƙa taskance bayanan ne a Rumbun Tara Bayanan Kuɗaɗen Haraji da ke liƙe da lambar shaidar katin ɗan ƙasa, wato lambar NIN.
A yayin taron da suka yi ranar Laraba, Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta karɓi kwafen Rahoto daga Shugaban Hukumar Tara Kuɗaɗen Haraji ta Ƙasa (FIRS).
Shugaban kuma shi ne Shugaban Kwamitin Haɗakar Tarayya da Jihohi na Tara Haraji, Muhammad Nami.
Sun karɓi rahoton ne dangane da yadda tsarin karɓa da tara haraji na D4T zai yi nasara sosai.
Gwamnonin sun nuna goyon bayan su kan shirin, wanda idan aka fara aiki da shi, aƙalla zai ƙara sa a tashi kashi 90 bisa 100 na sama da abin da ake karɓa daga kowane mai biyan haraji.
Sun ce za su haɗa kai da Kwamitin JTB domin ganin an samu ƙarin kuɗaɗen shiga da nunki biyu, ta hanyar nunka wa mutane haraji kashi 200%.
Waɗannan bayanai su na ƙunshe ne a cikin takardar bayan taron da Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi ya sa wa hannu, kuma aka raba wa manema labarai bayan ta.
A wurin taron, gwamnonin sun karɓi rahoto daga jagoran Tsarin Abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Babban Sakataren Ma’aikatar Kuɗaɗe da Tsare-tsare, Olusola Idowu, a kan Tsarin Inganta Abinci Na Ƙasa.
Discussion about this post