• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Yadda Tinubu ya taimake ni na zama gwamnan Jigawa -Badaru

    Crisis in Jos

    BAUCHI: Matasa sun babbake gidaje da shaguna da dama a Warji bayan Rhoda Jatau ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW

    GUDUN YIN BIYU-BABU: Gwamnan Bauchi ya sayi fam ɗin sake yin takarar gwamna, daidai lokacin da ya fito takarar shugaban ƙasa a PDP

    Farin jinin Buhari da mara min baya da yayi ya sa na samu daukaka a siyasa – Bala Mohammed

    Kano State Assembly

    Dan majalisar dokoki na jihar Kano ya doka ‘Ribas’ bayan ya tsunduma lambun jam’iyyar NNPP, ya ya rungumi tsintsiyar sa ya dawo APC

    Yadda EFCC ta damke Akanta Janar din Najeriya bisa zargin harkallar naira biliyan 80

    Dalilin da ya sa Buhari ya dakatar da Akanta Janar ɗin da ake zargi da kantara satar naira biliyan 80

    Nigerian Pilgrims

    HAJJIN BANA: Duk wanda ya zarce shekaru 65 bashi ba Hajji bana – Hukumar Alhazai

    Beggars

    Almajirai da mabarata sun kwararo Abuja – Mahukunta

    HARƘALLAR KWANGILA: EFCC ta kama Patricia Etteh, tsohuwar Kakakin Majalisar Tarayya

    Ƴan bindiga sun ƙona hedikwatar karamar hukumar Idemili ta Arewa a jihar Anambra

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    CHAMPIONS LEAGUE: Ko dai tsinuwar Yaya Toure ta yi tasiri kan Pep Guardiola?

    PILLARS SUN KIRA RUWA: Daga yanzu a Abuja za su rika wasan gida kuma an zaftare musu maki 3

    Yadda Kanawa suka yi ragaraga da motar ƴan  Katsina United saboda Pillars ta buga kunnen doki a Kano

    GHANA vs NAJERIYA: Ko Najeriya za ta kauce wa ɗauko buhun kunya na 26 a hannun ‘Black Stars’?

    Barcelona ta yi wa Madrid dukan kabarin kishiya, ba sani ba sabo ta zura mata kwallaye 4 babu ko ɗaya

    ‘CHAMPIONS LEAGUE’: Yadda Benzama ya ceto Madrid daga rijiya gaba dubu, ya kori PSG kuma ya dawo da martabar sa a duniyar ƙwallo

    YAƘIN UKRANIYA YA CI ƘUNGIYAR CHELSEA: ‘Zan sayar da kulob ɗin na sadaukar da kuɗin ga tallafin waɗanda yaƙin Ukraniya ya kassara’ -Abramovich, mai ƙungiyar kuma ɗan asalin Rasha

    RASHA: FIFA da UEFA sun dakatar da ƙungiyoyin Rasha buga wasannin ƙwallon Turai da duniya baki ɗaya

    KYAUTAR NAIRA MILIYAN 2: Allah ya saka wa Ahmed Musa, ina kira ga ‘yan wasa na yanzu su yi tattali don gaba – Obiekwue

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    KURUNKUS: Malami ya fito takarar gwamnan Kebbi, ya ce jama’ar jihar ne suka tilasta masa ya fito

    2023: Ɗan takarar shugaban kasa, Rotimi Amaechi ya ziyarci masarautar Dutse

    LABARI CIKIN HOTUNA: Yadda ƴaƴan jam’iyyar APC da dubban mutanen Kaduna suka yi wa Sanata Uba Sani goma ta arziki

    BIDIYO: Shin zaka iya zama da mai dauke da cutar Kanjamau? – Ra’ayoyin mutane

    Dalilin da ya sa muka yi tattaki har Dubai domin taya Aisha Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar ta – Matan Gwamnonin Najeriya

    BIDIYO: Yadda ‘yan bindiga suka rika jibga ta kafin a biya naira 50,000 kudin fansa – Dattijo Saidu Dabo

    ‘Yan mata marasa aure sun fi matan aure amfani da magungunan takaita Iyali – Ma’aikatar Lafiya

    BIDIYO: Kwalaben ruwan maganin rigakafin Korona sama da Miliyan daya da aka lalata a Abuja saboda sun gama aiki kafin a dirka wa ‘yan Najeriya

    BIDIYO: RIKICIN BILLIRI: Yadda muka rasa ‘yan uwa da dukiyoyin mu a rikicin sarauta – Galadiman Tangale

No Result
View All Result

RA’AYIN PREMIUM TIMES: TAKARAR 2023: Ko dai Gwamnan CBN Emefiele ya fito ya yi magana, ko kuma ya yi murabus

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
February 21, 2022
in Babban Labari
0
RA’AYIN PREMIUM TIMES: TAKARAR 2023: Ko dai Gwamnan CBN Emefiele ya fito ya yi magana, ko kuma ya yi murabus

A duk lokacin da batun zaɓen shugaban ƙasa ya kunno kai tun daga bayan samun ‘yanci har zuwa yau, har ɓarkewar Yaƙin Basasa, a kullum tashin hankalin da ke lulluɓe ruɗanin zaɓen sai ƙara muni ya ke yi.

Ta shiyyoyi da yankuna da dama tantagaryar ‘yan takifen maɓarnata da makasa ne sun tsare ƙofar shiga farfajiyar dimokraɗiyyar mu. A mafi yawan yankunan Arewa har zuwa Kudu, ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga da ‘yan takife ne ke amfani da muggan makamai su na ƙoƙarin ganin sai sun kassara ƙasar nan. A lokaci ɗaya kuma su na ƙoƙarin sai sun durƙusar da tattalin arzikin ƙasar nan.

Ko ta ina a cikin ƙasar nan ana fama da rayuwar ƙunci da tsada. Ga matsalar rashin aikin yi sai ƙara ta’azzara ta ke yi. Fatara da talauci sai ƙara katutu su ke yi. Ƙarin abin takaici shi ne yadda farashin kusan komai ke ƙara hauhawa a ƙasar nan.

Romon-kunnen da aka yi kwanan nan aka ce malejin tattalin arziki ya cilla sama, ya ɗan bunƙasa, to cirawa saman da ya yi ba zai iya sa tatttalin arzikin ya yi tashi ba, kai ko gwauron numfashi ma ba zai iya yi ba.

Daɗin daɗawa kuma a daidai wannan lokaci da ake ta kiki-kaka da ƙadabolon yadda Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta kasa fitar da kitse daga wuta, balle a samu rangwamen da ta yi alƙawarin samarwa, an fara tunanin wanda zai gaji kujerar shugaban Najeriya a shekara mai zuwa. Daga cikin masu hanƙoron ganin sun hau kujerar, wani mutum ɗaya da ya ɗauki hankalin wannan jarida, shi ne Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele.

Yayin da wasu ‘yan gararuma su ka fara ɓaɓatu da hayagagar cewa Emefiele ne ya cancanci zama shugaban ƙasa, saboda zai iya warware ƙabli da ba’adin da duk wata rabkanuwar da ta yi wa Najeriya da tattalin arzikin ta dabaibayi, PREMIUM TIMES na ganin cewa tatsuniya ce kawai ake yi, domin duk wata matsala da cukurkuɗewar da tattalin arzikin Najeriya ya yi, Godwin Emefiele ne ɗin nan ne dai Gwamnan Babban Bankin Najeriya, tun daga 2014 har zuwa yau.

Mafarki ne kawai ake yi da soki-burutsu, a ce wai mutumin da ya kai darajar naira cikin kwazazabon ramin da ta kasa fita, kuma a ce shi ne zai gyara Najeriya.

Yayin da Emefiele ya karya Dokar Aikin CBN, ya bi ruɗin jagaliyar ‘yan siyasa a matsayin sa na Gwamnan CBN, lamarin kamar akwai lauje cikin naɗi. Bai kamata Emefiele ya ci gaba da zama gwamnan CBN ba. Kuma bai kamata a kare shi ba ya ci gaba da zama gwamna, kuma ya na siyasa.

Idan Emefiele na so ya fito takarar siyasa don neman kowane muƙami, hankali da tunani da ya kamata sun nuna bai kamata ya ci gaba da riƙe muƙamin sa na Gwamnan CBN ba. Sannan kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa har yau bai nesanta kan sa daga masu haƙilo da hanƙoron masu neman ya zama shugaban ƙasa ba.

A kan haka ne PREMIUM TIMES ke yin kira ga Emefiele ya girmama muƙami da kujerar Gwamnan CBN, ya sauka daga muƙamin, ya je ya yi siyasar sa. Idan kuma babu ruwan sa da batun takarar sa, to ya fito ya nesanta kan sa, su daina, a wuce wurin.

PREMIUM TIMES ta haƙƙaƙe cewa muddin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fito ya fara neman kujerar shugaban ƙasa tun ya na kan aikin sa, to tabbas martaba da ƙimar wannan banki wanda shi ne ginshiƙin tattalin arzikin Najeriya, ta zube ƙasa warwas.

Dama kuma tun za zaɓen 2015 aka fara nuna damuwar cewa CBN ya shiga hidimar zaɓen shugaban ƙasa a zaɓen, da ma wasu zaɓukan baya.

Tags: AbujaEmiefileHausaLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

MATSALAR RASHIN FETUR: Ƙungiyar Ƙwadago ta TUC za ta tafi yajin aiki

Next Post

Dam ɗin ‘Rayfield Resort’ ya cinye ƙananan yara biyu a Jos

Dam ɗin 'Rayfield Resort' ya cinye ƙananan yara biyu a Jos

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda Tinubu ya taimake ni na zama gwamnan Jigawa -Badaru
  • Yadda iyaye na su ka yi hijira zuwa Jihar Adamawa – Atiku Abubakar
  • BAUCHI: Matasa sun babbake gidaje da shaguna da dama a Warji bayan Rhoda Jatau ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi SAW
  • FALLASA: An bankaɗo ɓoyayyar asusun ajiya na Jeremiah Useni a tsibirin Jersey wanda ya kimshe biliyoyin naira a lokacin yana ministan Abuja
  • RAHOTON MUSAMMA: Yadda Rigima ta ɓarke tsakanin Tambuwal da Hukumar WAEC kan kuɗin jarabawar ɗalibai

Abinda masu karatu ke fadi

  • Google on Masarautar Kano: Hassada Ta Sa Wasu Na Neman Wofintar Da Kokarin Su Danfodiyo! Daga Imam Murtadha Gusau
  • Kuşburnu Çekirdek Yağı on Dalilin da ya sa muka yi sallar Idi ranar Laraba a Bauchi, muka ki bin sanarwar Sarkin musulmi – Sheikh Dahiru Bauchi
  • Google on HARKALLAR BILIYAN 3.6: Ba nine Balan da ke jerin sunayen masu mallakin kamfanin Adda ba – Gwamna Bala
  • Google on SIYASAR ZAMFARA : Maitaimakawa tsohon dan takarar gwamna a APC akan harkar jarida ya sauya sheka
  • Google on RAMIN MUGUNTA: Yadda Boko Haram suka afkawa bam din da suka dana wa Sojojin Najeriya

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2022 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.