Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru ya bayyana cewa ya cika akalla kashi 94.8 cikin 100 na alkawuran da ya dauka a lokacin da yake neman zabe a jihar daga 2015.
Badaru ya fadi haka ne a taron karrama shi da kungiyar ‘Hadejia Ina Mafita’ ta yi ranar Litini a garin Hadejia.
Ya ce cikin alkawura 35 da muka dauka za mu yi a yankin Hadejia mun kammala 33 daga ciki zuwa yanzu.
Baya ga wadanda mutane suka bukaci mu yi, mun kirkiro wasu da dama wanda duk mun aiwatar da su akalla kashe 94 cikin 100 duk sun kammala.
“Yanzu shekara daya tal ya rage amma gwamnati za ta yi kokari wajen ganin ta kammala sauran aiyukan da ta dauka wanda ba a gama su ba.
Badaru ya mika godiyarsa ga mutanen Hadejia bisa wannan karramashi da suka yi.
A jawabin sa a wajen taron shugaban kungiyar Baidi Muhammad ya mika godiyarsa ga gwamna Badaru kan ayyukan ci gaba da ya aiwatar a yankin Hadejia.
“Gina babban asibiti domin inganta aiyukkan da babban asibitin Hadeja ke yi, inganta makarantar koyan harkokin noma zuwa kwalejin koyar da kimiya da fasaha na daga cikin manyan ayyuka da kungiyar ta bukata kuma gwamnati ta biya mata.
A Ƙarshe sarkin Hadejia maimartaba Adamu Abubakar ya mika godiyarsa ga gwamna sannan ya roki Badaru ya gina titin Hadejia zuwa Auyo.
Discussion about this post