Ministan Sadarwar Fasahar Zamani Isa Pantami ya yi magana a karon farko bayan Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa ASUU ta kira shi da cewa matsayin Farfesan da Jami’ar Fasaha ta Owerri FUTO ta ba shi haramtacce ne.
Pantami wanda ya yi magana a ranar Laraba, yayin da ya ke zantawa da manema labarai bayan kammala Taron Majalisar Zartaswa a Fadar Shugaban Ƙasa, ya ce ba zai ce komai ba, saboda taƙaddamar batun na kotu a gaban mai shari’a.
Yayin ganawar, Pantami ya yi cikakken bayani ne kan yadda Majalisar Zartaswa ta umarci dukkan jami’an gwamnati da hukumomin gwamnati su yi amfani da i-mel mai liƙe da alamar manhajar gwamnati.
Sai dai yayin da aka yi masa tambaya dangane da taƙaddamar cancanta ko rashin cancantar sa zama farfesa, ya ƙi cewa komai.
“Ba zan ce komai ba. Ba zan yi magana ba. Ba kuma zan yi magana ba. Na zo ne don na yi magana a kan abin da ya shafi ma’aikata ta. Saboda haka ba zan kauce daga abin da ya kawo ni nan wurin ku ba.
“Maganar nan ta na kotu. Kuma a matsayi na na jami’in gwamnati, na san laifin shiga hurumin kotu idan ba ta yanke hukunci kan shari’a ba. Kuma ni ɗan Najeriya ne mai bin doka da oda.”
A cikin Satumba 2021 ne Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri a Jihar Imo (FUTO) ta ɗaga likkafar daktoci 7 zuwa Farfesa, ciki har da Pantami.
Sai dai lamarin ya bar baya da ƙura, domin manyan masana da masu sharhin harkokin ilmi a ciki da wajen ƙasar nan, sun riƙa nanata cewa Pantami bai cancanta ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin matsayar ASUU, wato Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, wadda ta ce digirin-digirgir ɗin Minista Pantami na ‘Jami’ar Jatau Na Albarkawa’ ne.
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) sun yanke hukunci tare da ɗaukar matsayin cewa Digirin-digirgir na Farfesan da aka ba Ministan Sadarwar Zamani, Isa Pantami, haramtacce ne, don haka ba su yarda da shi ba.
Sun bayyana hakan ne bayan tashi daga taron su na tsawon kwanaki biyu da suka gudanar a Jami’ar Legas.
Majalisar Zartaswar ASUU ta ce ta bi diddigin yadda Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) ta bayar da muƙamin Farfesan Nazarin Kare Aikata Laifuka a Kafafen Sadarwar Zamani (Cyber security) cewa an kauce wa ƙa’ida da matakan da suka kamata ya bi kafin ya kai ga matsayin.
Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, Emmanuel Osodeke, ya ce:
“Majalisar Zartaswar ASUU ta yi Allah-wadai da matsayin ‘Farfesan’ da aka bai wa Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami.
“Daga hujjojin da muka tattara kuma muka tabbatar, Dakta Pantami bai cancanci muƙamin Farfesa ba. Sannan kuma ba shi matsayin ya kauce wa tsari, matakai da ƙa’idojin da ya kamata ya bi kafin ya zama farfesa. Kuma kowa ko a wace jami’a ce, sai ya bi waɗannan hanyoyi da matakai sannan ya ke zama farfesa a jami’a.
“Majalisar Zartaswar ASUU na kira ga dukkan mambobin ta da sauran rassan ƙungiyar na faɗin ƙasar nan, kada su amince kuma kada su riƙa bai wa Pantami girman da ake bai wa Farfesa.”
ASUU ta ce matsayin da ta ɗauka a yanzu ƙarin jaddadawa ce kan matsayin ta na farko da ta ɗauka cikin 2021.
Daga nan ta ce dukkan mambobin ta da su ke da hannu wajen cuku-cukun bai wa Pantami matsayin farfesa, za a hukunta su, don na baya su ɗauki darasi.
Discussion about this post