Mamallaka gidajen rediyo da talbijin da ke arewacin Nijeriya sun bayyana matuƙar damuwa dangane da ayyukan ‘yan ta’adda da mahara da sauran abubuwan assha da ke addabar yankin.
Don haka a ƙarƙashin Ƙungiyar Mamallaka Gidajen Rediyo da Talbijin ta Arewa (Northern Broadcast Media Owners Association, NBMOA) sun bayyana cewa za su fara wani aikin faɗakarwa ta hanyar kafafen su a kan wasu daga cikin munanan ayyukan da ke fuskantar Arewa da ma ƙasar baki ɗaya.
Ita dai NBMOA, ƙungiya ce ta mamallaka gidajen rediyo da talbijin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai a Arewa wadda aka kafa domin samun cigaban yankin da ƙasa baki ɗaya tare da tabbatar da ƙwarewa da bunƙasa a harkar aikin rediyo da talbijin a Nijeriya.
A lokacin da ya ke jawabi ga wani taron manema labarai da aka yi a Abuja a ranar Laraba, muƙaddashin shugaban ƙungiyar, Abdullahi Yelwa, ya ce ma’aikatan yaɗa labarai sun samu kan su a cikin mawuyacin hali dangane da rashin tsaro a Arewa.
Ya nuna cewa an cusa ƙasar nan cikin yaƙi da bala’in ta’addanci, ‘yan bindiga, kidinafin, rashin zuwan yara makaranta da kuma shaye-shayen muggan ƙwayoyi.
Ya ƙara da cewa wannan jerin ƙalubalen ya samu ne sakamakon fatara da kuma rashin cigaban al’umma.
A cewar Yelwa, gwamnati a dukkan matakai ta na yin iyakar ƙoƙarin ta domin ta daƙile waɗannan matsalolin saboda ta daidaita komai.
Ya ce an ɗauki matakai iri-iri, sannan an sawo sababbin kayan yaƙi na zamani waɗanda aka sanya cikin yaƙin.
Ya ce: “A kullum mu na fuskantar muggan abubuwan da waɗannan illoli su ke haifarwa a kan mutanen mu. A kullum ‘yan rahoton mu su na aiko da labaran hare-haren da ake kai wa ƙauyuka ana fatattaka su, sannan ana kama mutane ana garkuwa da su.
“A kullum mu na bada labaran yadda mahara ‘yan bindiga ke aika wasiƙu zuwa ga ƙauyuka da al’ummomi su na cewa a kai masu kuɗin fansa ko kuɗin neman izinin zuwa gonakin su. Mu kan ji yadda ake harbe mutanen da aka sace idan an kasa biyan kuɗin da za a ‘yanto su. Mu kan ji yadda gwamnoni su ke bayyana baƙin cikin su ko yadda yanzu wasu sassa na jihohin su ba su ƙarƙashin ikon su. Mu kan bada rahoto kan mutanen da a da su ke iya ciyar da kan su amma yanzu sun koma zaman dirshan a sansanin ‘yan gudun hijira.
“Kafafen yaɗa labarai na Arewa su na kan gaba wajen kawo rahotanni game da waɗannan matsaloli. Hasali ma dai wasu daga cikin membobin ƙungiyar mu sun sha wuyar wannan hali da ake ciki na ta’addanci, a yayin da a kullum mu ke faɗakarwa kan a kyautata wa mayaƙan mu da kuma waɗanda rashin tsaron ya shafa. Za mu ci gaba da sauke nauyin mu na tabbatar da nuna wa gwamnati abin da ya dace ta yi, tare da bada dama ga duk wani mai son ya faɗi ra’ayin sa kan yadda za a samo mafita kan tabbatar da tsaro a Arewa da Nijeriya baki ɗaya.”
Daga nan shugaban ƙungiyar ya bada sanarwar cewa daga yanzu sun ɗaura yaƙin faɗakar da jama’a kan wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar Arewa.
Yelwa ya ce, “A ci gaba da ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da rashin tsaro tare da bada gudunmawa ga nemo hanyoyin da za a samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da arziƙi a yankin mu da ƙasar mu, ƙungiyar mu ta NMBOA ta na sanar da jama’a cewa ta fara yekuwa ta kafofin ta a kan wasu daga cikin manyan matsalolin da ke addabar al’ummar mu.
“Tsarin da za mu bi shi ne za mu yi amfani da inda mu ke shiga da fita da kuma hanyoyi daban-daban da ke faɗin Arewa da ma wajen ta, mu yi magana da hukumomin gwamnati a dukkan matakai, tare da ƙungiyoyi masu zaman kan su, da sarakuna da shugabannin addini da muhimman masu ruwa da tsaki domin a samo ingantattun shawarwari na jama’a da yadda al’ummomi za su kasance su ne kan gaba wajen yaƙi da rashin tsaro.
“Ta hanyar tsara wasu shirye-shirye na musamman a tsanake, da tallace-tallace na musamman, da sauran su, za a ilmantar da masu saurare kan rawar da ya kamata su taka da kuma yadda abin da su ka yi ko su ka kasa yi ya ke taimakawa wajen samar da wani sakamako a wannan yaƙi kan rashin tsaro. Hakan ya kasance cigaba ne da haƙƙin jama’a da ya rataya a wuyan mu a matsayin mu na huɗu a jerin masu faɗa a ji a cikin al’umma.”