Shugaban majalisar tarayya, Femi Gbajabiamila ya umarci shugaban masu rinjaye na majalisar da ya gaggauta tattaunawa da ma’aikatar harkokin wajen Najeriya domin shirya yadda za a dawo da ƴan Najeriya daga ƙasar Ukraine da Rasha ta mamaye.
Gbajabiamila ya umarci Ado Doguwa ya tattauna da shugaban jiragen sama na Peace Air domin shirya yadda za a dawo da ƴan Najeriya gida.
Wani ɗalibi ɗan asalin Najeriya ya bayyana cewa sun wayi gari yau cikin tashin hankali da fargaba. Sun rika jin wucewar rokoki ta saman gidajen su da Rasha ke cillawa zuwa kasar Ukraine da duke kusa da jigar da yake zaune.
Kasar Rasha ta mamaye wasu sassa na kasar Ukraine tun daga ranar Alhamis inda ta rika yi wa kasar Luguden wuta ta sama bayan ta aika da sama da sojojinta 200,000 zuwa iyakan kasar da manyamanyan tankokin yaki
A rahotanni da ke bayyana daga ƙasar Ukraine an rika ganin yadda rugugin wuta na nakiyoyi da igwa igwa ta sama da kasa da sojojin kasar Rasha ke aikawa kasar Ukraine ɗin.
Gwamnatocin ƙasashe da dama sun tofin Allah-Tsine ga wannan harehare na sojojin Rasha akan kasar Ukraine.
Kasashen duniya ciki har da Amurka, Birtaniya, Faransa da sauran manyamanyan kasahen duniya na gargaɗin Rasha ta shiga taitayinta sannan sun bayyana cewa lallai za su saka wa kasar takunkumi masu tsauri da zai yi lagalaga da tattalin arzikin kasar.
Zuwa yanzu farashin ɗanyen man fetur ya yi tashin gwauron zabi a dalilin wannan mamaya da Rasha ta kaiwa Ukraine.
Discussion about this post